
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa, SDP ta kori tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30 bayan samunsa da laifin saɓa wa dokokinta da na zaɓe.
Bayanin hakan na ƙunshe a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, wadda ya fitar ranar Litinin, inda ya ce SDP ta ɗauki matakin ne a ƙarƙashin dokoki da tsare-tsaren jam’iyyar da kuma sashin dokar zaɓe na ƙasa da ya ba ta damar zaɓar wanda ta ke so ya zama mambanta.
Jam’iyyar ta kuma gargaɗi mambobinta a faɗin Nijeriya da kada su ƙulla wata alaƙar siyasa da shi tunda a yanzu shi ba mamba ba ne koma ba ya baya cikin masu wakiltar ta a kowane mataki.
Haka kuma, jamiyyar ta nemi Hukumar Zabe (INEC) da hukumomin da lamarin ya shafa su shaida cewa El-Rufa’i daga yanzu ba ɗanta ba ne har sai ranar 28 ga Yulin 2055.
Kazalika, takardar ta bayyana cewa kwamitin ayyukan jam’iyyar ya gano cewa El-Rufa’i bai yi rajistar zama mamba acikinta ba saidai yana ikirarin shi ɗan SDP ne wajen shiga a dama da shi a harkokinta.
