
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga Jihar Benuwai sun ce jami’an ƴan sanda sun yi nasarar ceto ɗaliban Makarantar Lauyoyi na reshen Yola guda shida da aka yi garkuwa da su a ranar 26 ga Yuli, 2025 a lokacin da suke hanyar komawa Jihar Adamawa daga Anambara.
A daren ranar Asabar wayewar Lahadi ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin iyakar Wukari a Jihar Taraba da Jihar Benuwai.
Kakakin rundunar ƴan sandan, Edet Udeme a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, ta ce an ceto ɗaliban cikin aminci.
Haka kuma, an miƙa su ga iyalansu a safiyar Juma’a, 1 ga watan Agusta, 2025.
Ta ƙara da cewa, jami’ansu na cigaba da aiki tuƙuru wajen bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma tsaro a faɗin sassan ƙasar.
