An gudanar da addu’ar Yaumul Shukr a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kamar yadda aka saba a kowace shekara, gwamnatin Jihar Katsina ta shirya babban taron addu’a da ake kira Yaumul Shukr domin nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa ni’imomin da ya yi wa jihar da kuma roƙon zaman lafiya da ci gaba a tsakanin al’umma.

An gudanar da wannan taro a babban masallacin Juma’a na Danfodiyo da ke Modoji, kusa da gidan gwamnatin Jihar Katsina.

Taron ya samu halartar fitattun malamai da shugabanni daga manyan ƙungiyoyin addini da suka haɗa da ɗarika, izala, ƙur’aniyyun, da sauran ƙungiyoyin addinin Musulunci.

Yaumul Shukr na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Katsina ke ɗauka da muhimmanci, domin tunawa da haɗewar tsoffin lardunan Katsina da Daura wani babban ci gaba da jihar ke ganin ya cancanci a gode wa Allah a kansa tare da roƙon ci gaba da zaman lafiya.

A jawabin rufe taron, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamna Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa wannan rana na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a jihar.

“Manufar wannan taro shine mu gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi mana, mu roƙi kariya da zaman lafiya, da kuma sabunta alƙawarin mu na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin gaskiya da adalci,” in ji Faskari.

Ya kuma jaddada buƙatar ci gaba da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin addini, yana mai kira ga malamai da su ci gaba da wa’azi mai gina ƙasa da ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin jama’a.

Taron Yaumul Shukr na ci gaba da zama muhimmin abin tunawa a jadawalin ayyukan jin ƙai a Jihar Katsina, inda ake samun dama ta musamman domin yin addu’o’i, tunani, da kuma neman shiriyar Allah ga gwamnati da al’ummar jihar gaba ɗaya.

By ukarofi