Mene ne laifin ’yan jaridarmu na cikin gida?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Muhawara ta ɓarke tsakanin ’yan Nijeriya, musamman mazauna arewacin ƙasar nan, dangane da kwarmaton da ɗan jaridar nan, kuma ɗan gwagwarmaya, Dr Bello Galadanci da aka fi sani da ɗan Bello ya yi, dangane da halin da wasu makarantun gwamnati a Jihar Kano ke ciki. A dalilin wannan bidiyon da ɗan Bello ya yi na fallasa halin taɓarɓarewar da ilimi ke ciki a Jihar, wanda ya watsu a kafofin sada zumunta, an ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da tawagarsa sun ziyarci wasu daga cikin makarantun da aka ambata, tare da ba da umarnin gyara su. Abin da ya jawo wa Gwamnan yabo da jinjina, a maimakon suka da Allah wadai.

Sai dai kuma bayan tiya akwai wata caca, in ji ’yan salon magana. Domin kuwa ɗaukar matakin gaggawa da Gwamnan ya yi da nufin shawo kan matsalar ta sosa zuciyoyin wasu ’yan jarida a ciki da wajen Jihar Kano, waɗanda ke ganin shugabanni da ‘yan siyasar ƙasar nan, musamman masu riƙe da madafun iko ba sa mutunta ’yan jarida na cikin gida. Saboda duk surutun da ake yi ta kafafen watsa labarai a cikin rahotanni da hirarraki game da halin da ilimin Jihar Kano ke ciki, Gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da ake yi. Sai yanzu da wannan ɗan kwarmato, ɗan Bello ya zo ya yi wannan bidiyo, shi ne suka tashi jiki na rawa don magance matsalar.

Wannan ba yana nufin wai Gwamnatin Jihar Kano ba ta damu da harkar ilimi ba ne, ko kuma ba ta da kyawawan tsare-tsare na inganta Ilimi ba, a’a. Bilhasali ma, Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, na daga cikin gwamnonin ƙasar nan da aka yaba da gudunmawar sa a harkar ilimi. Domin har Shaidar Karramawa ya samu a wannan fanni, sai dai an ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai.

Manufar wannan rubutu shi ne, tattauna batun yadda shugabanni a ƙasar nan ke fifita ’yan jaridar ƙasashen waje ko masu kwarmato a kafafen watsa labarai, fiye da asalin ’yan jarida ƙwararru na cikin gida, da ke aiki ba dare ba rana, domin tattara rahotanni da bayanai kan ayyukan da suke yi ga jama’a, domin duniya ta san irin ƙoƙarin da suke yi. Ba tare da yaba musu ko kyautata albashin su, da yanayin yadda suke gudanar da aikinsu ba.

Hatta a wajen ƙoƙarin neman ganawa da wani shugaba don yin wata hira ko neman fayyace wani bayani da ya shafi rahoton da ɗan jarida ke shiryawa, sai ka ga an ajiye mutum ko a yi ta juya shi, ana masa jeka ka dawo. Amma da zarar an ce, wannan ɗan jarida daga wata kafa ta waje yake kamar BBC ko Muryar Amurka da sauran su, lamarin ba haka yake ba. Hatta ɗan abin hasafi na sallama da aka saba bayarwa wani lokaci, nasu daban yake. Kulawar da ake basu da haɗin kan da suke samu a wajen shugabanni mu da muke tare da su a gida ba sa ba mu haka. Kodayake dama an ce ido wa ka raina, ya ce wanda nake gani kullum.

Ko a cikin gida Nijeriya ma, kulawar da ake bai wa kafafen watsa labarai na Kudu ba ɗaya ba ne da takwarorinsu na Arewa, ballantana uwa-uba ’yan jaridar turanci da na Hausa. Ana ganin darajar su ba ɗaya ba ce, sai an ga dama ake ba su haɗin kai ko amsa gayyatar su zuwa wani shiri ko wata hira. Haka kuma za ka ga irin manyan tallace-tallace da ake bai wa jaridu da kafafen talabijin na Kudu, namu na Arewa ba sa samun haka.

Yana faruwa ma a wajen neman damar gudanar da wani bincike na musamman wanda ke buƙatar sahalewar hukumomi, sai ka ga ɗan jaridar wata kafar watsa labarai daga waje ya shigo Nijeriya ya nemi a bashi dama zai gudanar da bincike kan wani abu da ya shafi tsaro ko zamantakewar al’umma. Ba tare da samun wani tsaiko ko wata tangarɗa ba, sai nan da nan a amince masa har ma da samar masa da ɗan rakiya. Amma ɗan jaridar cikin gida ba ya samun wannan gatan, wani lokaci ma in bai yi dace ba, har yunƙurin kama shi ko kashe shi za a yi idan ya matsa da bincike kan wani batu da ake so a yi wa rufa-rufa. Mun ga yadda wasu daga cikin abokan aikin mu rayuwa ta yi da su.

A lokacin da rigimar Boko Haram take tsakiyar ganiyar ta mun ga yadda ake takura fitar da bayanai ga ’yan jaridar mu na gida, amma abin mamaki sai ka ga ’yan jaridar ƙasashen waje suna shigowa suna naɗar rahotanni suna tafiya babu wani mai ƙwarzabarsu. Nasan ba za ka manta da rahoton da wani ɗan jaridar BBC ya haɗa game da halin da ’yan bindigar daji a jihohin Zamfara da Sakkwato ke ciki ba, dangane da satar ɗalibai ’yan makaranta da suke yi. Sai bayan da rahoton ya fita har jama’a suka fara ƙorafi da sukar gwamnati akan saken da ta yi har waɗannan bayanai suka fita a kafafen sadarwa, shi ne aka dakatar da watsa shi. Idan kuwa da wata kafa ce a cikin gida ta shirya wannan rahoto, mutane da yawa za su iya fuskantar barazanar rasa aikinsu.

Lallai ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su canza salon yadda suke hulɗa da ’yan jarida na cikin gida da suka fi kusa da su. Su ƙara ba su haɗin kai da kulawa a lokacin da suke bakin aiki, domin suna yi ne don kare martabar su da kimar jami’an gwamnati a idon jama’a. Sannan su sani cewa, zargin kwaɗayi da sa rai da abin hasafi da wasu ’yan jaridar ke yi yana da nasaba ne da sakacin gwamnati da ’yan majalisa, na rashin samar musu da kyakkyawan albashi. An mayar da ɗan jarida a Nijeriya kamar Almajiri, saboda ba ya samun abin da zai kula da buƙatun iyalinsa, sakamakon rashin kyan albashi. A kafofin watsa labarai masu zaman kansu ma, abin ya fi muni, don a wasu kamfanonin alawus ɗin da ake basu ko kuɗin mota ba ya isar su, balle a je ga batun abinci.

Lallai aikin jarida a Nijeriya yana fuskantar ƙalubale mai yawa, da ya kamata gwamnati da masu ruwa da tsaki daga wakilan ƙungiyoyin ’yan jarida na NUJ da RATTAWU, su yi wani yunƙuri don ganin an samar wa aikin jarida kima da martabar da ya kamata ya samu, a matsayin sa na turke na huɗu na tsarin dimukraɗiyya.

Sannan ga ’yan siyasa da masu mulki, su gane akwai bambanci tsakanin ɗan jarida mai lasisi wanda ya samu horo da ƙwarewa, da kuma mai yawo da waya yana ɗauke-ɗauken hoto yana watsa wa a kafafen sadarwa na zamani, don yaɗa manufofin ɗan siyasar da yake goyon baya. Abin kunya ne da takaici ’yan siyasa su riƙa fifita waɗannan yara da suke kira ýan Midiya a wajen su, akan sauran ’yan jarida na asali da ke aiki da dokoki da ƙa’idojin aiki, bisa tsarin dokar ƙasa. Alhalin su waɗannan yara ko cikakken karatu ba su yi ba, kuma ba su da ilimi kan abin da ya dace da wanda bai kamata ba a harkar watsa labarai.

Ina kira ga hukumomi da waɗanda abin ya shafa su tashi tsaye da kyau su yi abin da ya kamata, don kare mutuncin aikin jarida a ƙasar nan.

By ukarofi