
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ƙara sati guda ga wa’adin neman aiki a wasu hukumomin tsaro.
Hukumomin sun haɗa da Hukumar Shige da Fice (NIS) da Civil Defence (NSCDC) da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCos) da kuma Hukumar Kashe Gobara (FFS).
Hukumar gudanarwar haɗakar hukumomin ta sanar da haka a wata takarda daga Sakatarenta, Manjo Janar Abdulmalik Jibril (mai ritaya) a Abuja, ranar Lahadi.
Da fari an tsara rufe shafin neman gurbin aikin ne a ranar 4 ga watan Agusta, 2025, inda a yanzu aka mayar da shi ranar 11 ga wata.
Ya ce, an yi haka ne da nufin bada dama ga ƙarin masu ƙoƙarin neman aiki a hukumomin shiga sahun waɗanda suka miƙa bayanansu na neman ayyukan.
Haka kuma, ya tunatar da masu shirin neman sahihin shafin da aka amince da shi a hukumance, wanda shi ne; htpps://recruitment.cdcfib.gov.ng.
Kazalika, ya jaddada cewa ba a biyan kuɗi a yayin bin hanyoyin neman aikin, sannan suna aiki tuƙuru wajen tabbatar da gaskiya da adalci acikin haka.
