
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana zargin Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Bayo Ojulari ya yi murabus a matsayin abinda ta kira da ‘ƙarya kuma shirme’.
Da ya ke ganawa da jaridar DAILY POST, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Sunday Dare a ranar Asabar, ya ce babu gaskiya akan cewa an tilasta wa Ojulari rubuta takardar murabus.
Ya yi ikirarin lamarin wanda ya auku a daren ranar Juma’a wayewar Asabar ya ƙunshi Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC Ola Olukoyede da Darakta-Janar na DSS Adeola Ajayi.
Muryoyi sun shaida wa manema labarai cewa EFCC ba ta yi garkuwa da Ojulari ba, batun da suka bayyana a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
Haka kuma sun ce, Olukoyede bai da buƙatar yin garkuwa ko tilasta wa wanda gwamnati ta naɗa yin murabus, saboda a hukumance bai da ikon yin haka.
Al’amarin shugabancin Ojulari ya soma shiga tsaka-mai-wuya ne a lokacin da ya je babban taron masu ruwa da tsaki kan harkar mai a Kigali tare da wata tawaga da NNPC ya ɗauki nauyinsu.
