NBC kaɗai ke da alhakin rufe gidan rediyo – Ministan Labarai kan rufe Badeji FM a Jihar Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwmanatin Tarayya ta yi tsokaci akan umarnin Gwamnan Neja, Umaru Bago na a rufe gidan rediyon ‘Badegi FM’ mai zaman kansa a Minna, Babban Birnin jihar, bisa zargin sa da nuna rashin Kware wajen gudanar da harkokinsa.

A sanarwar da Mai taimaka wa Ministan Labarai, Mohammed Idris akan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar ranar Juma’a, Ma’aikatar ta nuna damuwa kan yadda ƙungiyoyi masu zamani kansu suka koka game da faruwar al’amarin.

Gwamna Bago ya bada umarnin ne a lokacin da jam’iyyar APC take gudanar da babban zama da ya ƙunshi jiga-jiganta, wanda Ministan Labaran na ɗaya daga cikin waɗanda suka halarta.

Yayin da Ma’aikatar ke tsokaci kan al’amarin, ta ce lamarin da ya shafi rufewa ko ƙwace lasisin gidajen yaɗa labarai ya rataya ne a wuyan Hukumar Kula da Gidajen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC).

Haka kuma, Ma’aikatar ta yaba wa gwamnatin jihar Neja kan miƙa al’amarin ga NBC domin ɗaukar matakan da suka dace a kai.

Kazalika, Ministan ya yi kira da a kwantar da hankula kan al’amarin yayin da NBC ke ƙoƙarin aiki da hukuncin doka domin shawo kan al’amarin.

By Babaji