Masarautar Katsina ta naɗa Sirika da ɗan Gwamna Raɗɗa a matsayin hakimai

Spread the love

Daga UMAR GARBA Katsina

Masarautar Katsina ta sanar da naɗa tsohon ministan marigayi Buhari da ɗan gwamnan jihar ta Katsina da kuma wasu mutum huɗu a matsayin sababbin hakimai a Katsina.

An bayyana sababbin hakiman ne cikin wata sanarwa da sakataren masarautar, Alhaji Bello Iro ya fitar ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025.

A cewar sanarwar, masarautar Katsina ta amince da naɗin Sanata Hadi Sirika a matsayin sabon Marusan Katsina, Hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi. Hadi Sirika dai ya yi aiki a matsayin ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Muhammad Dikko Raɗɗa, ɗan gwamna Dikko Raɗɗa, shi ne sabon Gwagwaren Katsina, Hakimin Raɗɗa a ƙaramar hukumar Charanchi, sauran sababbin hakiman da aka naɗa sun haɗa da:
Alhaji Sanusi Kabir Usman, Karshin Katsina, Hakimin Shinkafi a ƙaramar hukumar Kaita.
Alhaji Ahmad Abdulmumini-Kabir, Ɗan-Majen Katsina, Hakimin Dankama, a ƙaramar hukumar Kaita. Alhaji Abubakar Dardisu, Sarkin Mudurun Katsina, Hakimin Muduru, a ƙaramar hukumar Mani.
Alhaji Gambo Abdullahi Dabai, Dausayin Katsina, Hakimin Dabai, a ƙaramar hukumar Ɗanja.

Masarautar ta Katsina ta ƙara da cewa naɗin sababbin hakiman ya fara aiki ne daga ranar Asabar.

By ukarofi