Kujerar Shugaban NNPC ta fara rawa bisa zargin badaƙalar Dala miliyan 21 – Rahoto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ana fargaba akan shugabancin fannin mai a Nijeriya yayin da aka bijiro da rahoton cewa an tilastawa wa Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari yin murabus daga muƙamin a sakamakon matsi daga jami’an hukumar (EFCC), kamar ya jaridar News Point Nigeria ta ruwaito.

Muryoyi da dama da ba a tabbatar da su ba, sun bayyana cewa, matsin yin murabus ɗin bai samu amincewar Fadar Shugaban Ƙasa ba, amma Shugaban EFCC, Ola Olukoyede da Darakta-Janar na ƴan sandan farin kaya (DSS) Adeola Ajayi sun yi ƙoƙarin tabbatar da hakan.

Saidai, Fadar Shugaban Ƙasa ta bakin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga a ranar Asabar, ta tabbatar da cewa har yanzu Ojulari ne shugaban babban kamfanin man.

A watan Afrilun 2025 aka naɗa Ojulari, wanda tun daga lokacin ya fara ƙoƙarin inganta tsayar da gaskiya da adalci a fannin mai a Nijeriya, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Al’amarin da ya haddasa cecekucen ya samo asali ne akan wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai kimamin Dala miliyan 21 (N34.65bn) na rashawa da ya ƙunshi ƴan kasuwa a fannin da ƴan kwangila a tashoshin mai.

Tuni ƙungiyoyi masu zaman kansu da tawagar OilWatch Nigeria gami da Haɗakar ƙungiyar kare ƴancin ma’aikata suka nemi a kama Ojulari, bayan da Abdullahi Bashir Haske da aka kama da hannu a riƙe da haramtattun kuɗaɗen ya yi zargin cewa ya yi hakan ne a madadin Ojulari.

Haka kuma, a ranar 31 ga Yuli a Hedikwatar EFCC, haɗakar ƙungiyoyin suka zargi Ojulari da yin zagon-ƙasa ga harkar tattali inda a cewarta, yana rufe matatun man ƙasar da wasu kadadorin NNPCL da nufin shirin sayer wa ƴan kasuwa.

By Babaji