
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani rahoton sirri da hukumar ƴan sandan farin kaya (SSS) ta fitar, ya zargi Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Ibrahim Namadi da karɓar cin hancin Dala 30,000 daga Sulaiman Ɗanwawu, wanda babban dillalin ƙwaya ne, domin tsaya masa a kotu.
A cewar muryoyi da dama a Abuja, SSS ta gudanar da ja musamman game da lamarin inda ta shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sallami kwamishinan bisa zargin sa da hannu a laifin.
Namadi wanda a bayan an same shi da hannu a aikata manyan laifuka ciki har da ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo a shekarar 2013, an naɗa shi a muƙamin ne bisa alfarmar mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso duk da fari gwamna yana da wata matsa akan haka.
Lamarin ya biyo bayan da kwamishinan ya sanar Babbar Kotun Tarayya da ke Kano muradinsa na tsaya wa dillalin ƙwayar a ranar 18 ga Yuli, bayan da ta nemi Ɗanwawu ya samo mutum ɗaya da zai tsaya masa a matsayin sharaɗin belinsa.
Baya ga haka kotun ta nemi a biya Naira miliyan 5 a asusun banki da ke ta’ammali da riba (interest).
An samu cecekuce acikin al’umma a lokacin da Namadi ya ƙudirin aniyarsa ta tsayawar musamman akan harkokin siyasa a jihar Kano.
Haka kuma, al’amarin ya jefa Gwamna Abba Kabir Yusuf halin tsaka-mai-wuya, inda wasu ke ganin abinda kwamishina ya aikata ne ya sanya shi a halin, lamarin da ya sa ya yi zama da masu-ruwa-da-tsaki da kuma shawartar Kwankwaso da jigon jam’iyyar NNPP da ya bada sunansa a muƙamin kwamishinan.
