Daga USMAN KAROFI a Abuja
Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Kano mai kula da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma ya kai ziyara ƙaramar hukumar Dawakin Tofa domin duba ayyukan da shugabancin ƙaramar hukumar ya aiwatar.
A yayin ziyarar, kwamitin ya zagaya wurare daban-daban don bibiyar manyan ayyukan ci gaba da aka gudanar a yankin, waɗanda suka haɗa da ayyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sahale wa ƙaramar hukumar, da kuma waɗanda ƙaramar hukumar ta yi da ƙashin kanta.
Ayyukan sun haɗa da gina sababbin asibitoci da gyaran tsofaffi, gyaran makarantu, gina magudanan ruwa, da sabunta sakatariyar Dawakin Tofa gaba ɗaya.
Shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Isma’il Jibrin Falgore, wanda Alhaji Tukur, ɗan majalisar jiha mai wakiltar Fagge ya wakilta, ya ce sun gamsu da irin nagartattun ayyuka masu ɗorewa da ake gudanarwa a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Anas Mukthtar Bello Ɗanmaliki.
A nasa jawabin, Danmaliki ya bayyana farin cikinsa kan yadda kwamitin ya yaba da ingancin ayyukan da suka gudanar a sassa daban-daban na yankin. Ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewa da kishin al’umma da yake nunawa wajen inganta rayuwar jama’a a faɗin jihar.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira ga al’umma da su kula tare da kiyaye ayyukan da gwamnati ta shimfiɗa, domin su amfani kowa da kowa na dogon lokaci.
