WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Cibiyar Kula da harkokin Jarrabawa ta Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da sako sakamakon jarrabawar ɗaliban da suka rubuta na wannan shekarar (wato 2025 WASSCE).

Hakan na ƙunshe a wata takarda da ta fitar, ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025.

Cibiyar jarrabawar ta sanar da cewa ɗaliban da suka rubuta jarrabawar za su iya duba sakamakonsu daga yanzu ta yanar gizo.

Ta kuma ce, hakan zai yiwu ne ta sahihin shafinta na https://waecdirect.org.

An fitar da sakamakon ne makonni kaɗan da suka gabata da ɗaliban suka kammala rubutawa a makarantu daban-daban da ke faɗin Nijeriya.

Kimanin ɗalibai guda 1,973,253 daga makarantu 23,554 da suka rubuta jarrabawar.

By Babaji