Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi Hon. Aminu Ibrahim ya gabatar da ƙudirin, inda ya nemi abokan aikin shi na majalisa da su mara mashi baya, a tunatar da ɓangaren zartarwa na jihar Katsina domin ɗaukan matakin gaggawa.
“Gwamnati ta ƙara ƙaimi tare da ƙarfafa tsaro, a yankunan Malumfashi da sauran ƙananan hukumomi dake fama da matsalar tsaro, dake a jihar,”inji ɗan majalisar.
Ya bayyana cewa suna sane da ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen samar da tsaro, amma dai a halin da ake ciki yanzu abubuwan sunyi ƙamari.
Ɗan majalisar ya bada misali da garuruwan Karfi, Ruwan Sanyi, Na-Alma da Lambun kyauta, inda yace a halin da ake a yanzu a karamar hukumar Malumfashi, akwai mazaɓar karfi da rana yan bindiga ke hare hare daga baya su yu awon gaba da mutanen yankin.
Hon Aminu Ibrahim Malumfashi ya buƙaci sauran ƴan majalisar su goyi bayan ƙudurin da ya gabatar domin a aikewa ɓangaren zartarwa ta ɗauki matakin gaggawa.
Haka kuma a zaman majalisar Hon. Muhammad Abubakar khamis mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma ya gabatar da ƙudiri inda ya buƙaci ɓangaren zartarwa da ta gina magudanan ruwa a unguwar Shema tare da sanya wutan lantarki mai amfani da hasken rana a Gagaren Wakafi zuwa layout.
Ka zalika haɗin gwiwa na yan majalisar ƙananan hukumomin sansani da Dutsi Hon Sale Magaji da
ƙaramar hukumar Sandamu Hon. Sale Magaji da Hon Abduljalal Isma’il sun buƙaci gwamnatin Katsina da ta binciki rikicin da ya faru tsakanin. Inda suka buƙaci ɓangaren zartarwa manoma da makiyaya a yankunan da har aka rasa rayuka.
‘Yan majalisar sun buƙaci ɓangaren zartarwa da ta aike da agajin gaggawa ga al’ummomin da rikicin ya shafa.
Bayan gabatar da ƙudurorin Kakakin majalisar dokokin wanda ya jagoranci zaman majalisar ya buƙaci akawun majalisar da ya turama ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.
