Legas: ‘Yan sanda sun gurfanar da sanannen makashi, Olori Eso kan manyan laifuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an ƴan sanda a Jihar Legas, sun yi nasarar cafke Wasiu Akinwande, wanda shahararren makashi ne da ya addabi wasu yankuna, inda suka gurfana da shi a wata kotun shari’a da ke yankin Ogba a jihar, bisa tuhumar sa laifuka 11 masu alaƙa da kisan kai, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da cin amanar ƙasa da sauransu.

Kakakin rundunar ƴan sandan, Benjamin Hundeyin ya bayyana haka a wata, ranar Talata.

Ya ce, Akinwande, wanda ya shahara da suna Olori Eso, shi ne ɗan ta’addan da aka fi nema ruwa-a-jallo, inda aka kama shi a yayin wani atisaye na musamman da aka yi wa laƙabi da ‘Silence Speed and Surprise’ da jami’ai na musamman suka ƙaddamar.

Hatsabibin ya shahara wajen addabar al’umma a yankin Mushin da kewaye, wanda har Jihar Ogun an je neman sa ba a yi nasarar kama shi ba.

Haka kuma, rundunar ta ƙwato tarin wasu muggan makamai da wasu ababen aikata manyan laifuka a gidan mai laifin, wanda ya amsa cewa da su ya ke amfani wajen gudanar miyagun ayyukan a duk lokacin da ya fita da ƴan dabarsa.

Daga cikin laifukan da ake tuhumar sa akansu akwai kisan Bankole Yusuf da Ramadan Yusuf a ranar 31 ga watan Yuli, 2024 a garin Mushin.

Sannan, a ranar 9 ga watan Disambar 2010, ya halaka wata ƴar shekara 10 mai suna Aminat Lateef a yankin Fadeyi da ke Legas da sauran manyan laifuka da ya aikata.

By Babaji