Gwamnatin Katsina ta raba sama da Naira miliyan 11 ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta raba tallafin kuɗi har naira miliyan 11 da dubu 250 ga iyalan da harin ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Bakori da Faskari.

Babban mataimaki na musamman ga gwamna kan lamuran waɗanda harin ƴan bindiga ya shafa da ƴan gudun hijira, Hon. Sa’idu Ibrahim Danja (Kogunan Jibia), ne ya jagoranci rabon kuɗaɗen a madadin gwamnati.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da iyalan waɗanda aka kashe, aka jikkata, aka sace ko waɗanda aka ƙona musu dukiyar su da dabbobin su.

Gwamnati ta ba iyalan jami’an tsaro da suka mutu naira miliyan ɗaya, iyalan ‘yan sa-kai da aka kashe naira dubu 500,000, na waɗanda aka jikkata ko aka kashe da ba jami’an tsaro ba naira dubu 200,000, na waɗanda aka sace naira dubu 100,000, yayin da waɗanda suka ji rauni suka karɓi naira dubu 50 bayan an biya musu kuɗin jinya.

Sakatariyar hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Hajiya Binta Husaini Dangani, ta jagoranci raba kayan tallafi da suka haɗa da buhunan shinkafa 50, wake 20, dawa 50, gero 8, masara 50, tabarma 200, man girki jarka 10, katunan magi 10, da gishiri buhu 10.

Wannan na daga cikin taimakon gaggawa da gwamnati ta tanada don rage wa jama’a raɗaɗin hare-haren.

Ɗan majalisar dokoki na jihar mai wakiltar Bakori, Hon. Abdurrahman Ahmad Kandarawa, ya yabawa wannan mataki na gwamnati, yana mai jaddada ƙudurin gwamnati na shawo kan matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma yi godiya ga gwamnatin Dikko Raɗɗa bisa ƙirƙirar dakarun Community Watch Corps domin ƙara samar da tsaro a yankin.

Ɗan majalisar ya roƙi waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata.

By ukarofi