
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar ambaliya a sassan jihohi guda 19 da kuma wasu wurare 76 a faɗin Nijeriya.
Gargaɗin da aka fitar daga Ma’aikatar Kula da Muhalli, ya buƙaci masu ruwa da tsaki da mazauna yankunan da lamarin ka iya shafa da su ɗauki matakan kariya.
Hakan na zuwa ne yayin da mummunar ambaliya ta afku a jihohin Ogun da Gombe yayin da wasu jihohin da suka haɗa da Legas da Filato da Anambra da Delta da suma matsalar ta shafe su.
A cewar sanarwar, ana hasashen yankunan za su samu mamakon ruwan sama da zai iya haifar da ambaliya daga 5 zuwa 9 ga watan nan na Agusta.
Jihohin da hasashen ya shafa sun haɗa da Akwa-Ibom da Bauchi da Ebonyi da Kuros-Riba da Nasarawa da Benuwai da Kaduna da Katsina.
Sauran sun haɗa da Kebbi, Kano, Neja, Filato, Taraba, Jigawa, Yobe, Zamfara, Sakkwato Borno da kuma Gombe duk a arewacin Nijeriya.
Matsalar ambaliya a Nijeriya ta zama ruwan dare kowace shekara wadda ke janyo asarar rayuka da salwantar dukiya mai yawa, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.
A shekara da ta gabata, jihohi 31 rahotanni suka bayyana sun yi fama da bala’in ambaliya da ta shafi mutum miliyan 1.2.
