Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin naira biliyan 4.2 ga ayyukan bincike 158 da ke ƙarƙashin Asusun Tallafawa Bincike na TETFund (NRF) na shekarar 2024.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na TETFund, Abdulmumin Oniyangi, ya fitar a Abuja.
Ya ce tantancewar da kwamitin nazari da sa ido na TETFund (NRFS&MC) ya gudanar ya biyo bayan karɓar bayanan ra’ayi 6,944 daga masana daban-daban a faɗin ƙasar.
A cikin adadin, ɓangaren Kimiyya, Fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire (SETI) ya samu mafi yawan kuɗi da ya kai naira biliyan 2.34, yayin da ɓangaren Harsuna da Kimiyyar Zamani (HSS) ya samu naira biliyan 1.02, sai kuma ayyukan da suka haɗa fannoni da dama (Cross-Cutting) da aka ware musu naira miliyan 870.7.
Manyan jami’o’in da suka fi cin gajiyar tallafin sun haɗa da Jami’ar Fasaha ta Minna da ke da ayyuka 15 da kuɗinsu ya kai naira miliyan 400.03, Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, da ayyuka 13 da kudin su ya kai naira miliyan 359.80, da Jami’ar Fasaha ta Akure da ke da ayyuka 12 da kuɗin su ya kai naira miliyan 341.60.
Wasu daga cikin muhimman ayyukan binciken sun haɗa da ƙirƙirar takin zamani da ke ɗauke da sinadarai masu amfani daga tsirrai, da kuma samar da jirgi mai sarrafa kansa don magance ciyawa da cututtuka a gonakin masara da wake.
Haka zalika, akwai kirkirar na’urar duba lafiya ya zamani don dakarun da ke filin daga.
A wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire, gwamnati ta kuma amince da kafa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci (Innoɓation and Entrepreneurship Hubs) guda 18 a makarantun da ke cin gajiyar TETFund a sassa shida na kasar nan.
Waɗannan cibiyoyi za su haɗa da ɗakunan gwaji irin su na lantarki, ƙirƙirar kayayyaki, da na’urar robot da kuma fasahar Artificial Intelligence.
Haka kuma, gwamnati ta ware kudade a cikin kasafin 2025 ga cibiyoyi 15 da suka hada da Jami’ar Dutse, Jami’ar Uyo, Jami’ar Ibadan da sauransu, inda kowane daga cikin su zai samu tsakanin naira miliyan 750 zuwa biliyan ɗaya.
