Daga AISHA ASAS
‘Sun tabbatar da cewa soyayya ba kawai da baki ake furtawa ba, sai da jajircewa da sadaukarwa’
A duk faɗin duniya, musamman a nahiyar Asiya, fina-finai sun daɗe suna taka rawar gani wajen bayyana labarai na zuciya, al’adu, ƙauna da gwagwarmaya. A sinimar Indiya da ta Tamil, fina-finai biyu sun fi fice wajen tabbatar da irin wannan tasiri, wato ‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’. Waɗannan fina-finai sun sauya fuskar sinima, sun gina wani sabon fahimta game da ƙauna da rayuwa, kuma har yau suna zaune a zukatan masu kallo, shekaru da dama bayan fitarsu.
Dilwale Dulhania Le Jayenge: Fim ɗin da ya mayar da soyayya ta sinima abin koyi:
Wanda ke da laƙabi na gajere DDLJ, fim ɗin ‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ wanda aka saki a shekarar 1995, ya zama wata alama ta ƙauna a sinimar Bollywood. Fitaccen lokacin da Simran ta ruga zuwa ga Raj yayin da jirgin ke barin tashar, ya shiga cikin jerin mafi shahararrun sahunan ƙarshe a tarihin sinima. Wannan bai tsaya kawai a matsayin salo na fim ba, ya zama alamar daurewar zuciya da jarumtar soyayya.
Fim ɗin, wanda Aditya Chopra ya fara jagoranta yana ɗan shekara 23, ya kasance wata gagarumar nasara. A karon farko, matasa sun ga wani salo da ya haɗa soyayya da tsananin girmama iyaye da al’ada. An nuna yadda ake zaune tsakanin buƙatun zuciya da ra’ayin dangantaka ta aure. Wannan haɗin zamani da gargajiya ne ya sa fim ɗin ya fi karɓuwa a kowanne mataki na al’umma.
Baya ga haka, wuraren da aka ɗauki fim ɗin, musamman shimfiɗar ƙasar Switzerland, sun ƙara daɗaɗa labarin suna bayyana marmarin ‘yanci da rashin takura. Har ma tufafin jaruman, daga rigar Raj zuwa zannuwan Simran, sun taka rawa wajen bayyana halayen su da matsayin su a rayuwa.
Kaakha Kaakha: Soyayya da rayuwa a cikin hatsarin aiki:
A cikin duniyar sinimar Tamil kuwa, fim ɗin ‘Kaakha Kaakha’ wanda aka fitar a shekarar 2003, ya bayyana wani sabon salo na fim ɗin ‘yan sanda. Gautam Vasudev Menon ya jagoranci fim ɗin, inda ya fitar da sabon salo na labarin rayuwa da aiki da kuma soyayya a tsakanin hatsarin aiki.
Suriya, wanda ya taka rawar Anbu Chezhiyan, ya bayyana jarumin dan sanda mai jajircewa amma kuma mai tausayi wanda ke fama da matsin lamba na aiki da kuma ƙaunar wata malama mai suna Maya (Jyotika). Soyayyarsu ta taɓa zuciya, bata tsaya ga shaƙatawa ko wasa ba, fim ɗin ya nuna soyayya cikin gaske da sadaukarwa.
Wani babban ginshiƙi na wannan fim kuwa shi ne kiɗan Harris Jayaraj, wanda waƙoƙinsa kamar Uyirin Uyire da Ondra Renda suka sanya fim ɗin cikin zuciyar masu kallo kuma da sauraro. Kiɗan bango da waƙoƙin soyayya sun ƙara faɗakarwa cikin nishaɗi.
Haka zalika, jarumin azzalumi Pandya, wanda Jeevan ya fito da shi, ya kasance tamkar ruwan dare a cikin labari. Ya haifar da juyin halin da ya jefa jaruman cikin gwagwarmaya, kuma daga ƙarshe, fim ɗin ya kawo ƙarshe mai cike da motsa rai da sarewar gwiwa.
Fina-finai irin su DDLJ da ‘Kaakha Kaakha’ sun tabbatar da cewa, sinima ba kawai nishaɗi ba ce, tana ɗauke da darussa, da falsafa, da saƙonni masu faɗakarwa. Duk da bambancin harshen da aka shirya su da yanayin da suka fito daga Indiya, ɗaya daga Tamil Nadu, duka sun nuna cewa ƙauna da sadaukarwa ba su da iyaka.
Masu shirya fina-finai sun bayar da gudunmawa wajen tsarkake zukatan jama’a, fadakar da al’umma, da kuma kawo sauyi ta hanyar nishaɗi mai ma’ana. A yau, shekaru 30 da DDLJ da kuma shekaru 22 da ‘Kaakha Kaakha’, har yanzu tasirin su yana nan ƙal-kal, yana cigaba da ratsa zukatan matasa da masu son fina-finai da ba sa wasa da saƙon zuciya.
‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’ sun zamo ginshiƙai ne na irin tasirin da soyayya da sadaukarwa ke da shi a sinima. Duk wanda ya kalli fim ɗin zai samu nishaɗi, darasi, da kuma tunani mai zurfi. Wannan ne ke tabbatar da cewa fim mai kyau, ko daga ina ya fito, zai iya karɓuwa idan ya taɓo zuciya.
