Shettima ya jagoranci tawagar Shugaban Ƙasa a ta’aziyyar Audu Ogbeh

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Fadar Shugaban Ƙasa a ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon Ministan Noma da Raya Karkara, Audu Ogbeh.

Ogbeh, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PDP a tsakanin 2001 da 2005, ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata bayan shafe shekaru 78 a duniya.

Shettima ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa masu hangen nesa, wanda za a cigaba da tuna irin gudumawar da ya bayar ga harkar tsaron abinci a tarihin raya ƙasa.

Ya ce, rashin Ogbeh zai haifar da babban giɓi ga harkokin inganta noma da ci-gaban ƙasa.

A sanarwar da Kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar a ranar Litinin, ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasar ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ne yayin jajenta wa iyalan marigayin da gwamnati da al’ummar jihar Benuwai bisa babban rashin da aka yi musu da ma ƙasa baki ɗaya.

A yayin ziyarar, Shettima ya gana da iyalan nasa tare da isar da saƙon ta’aziyyar Fadar Shugaban Ƙasa akan abin alhinin, yana mai jinjina wa ƙoƙarinsa ga harkar noma da ci-gaban ƙasa.

By Babaji