Daga AISHA ASAS
Mahaifa ce asali da ƙarfin jikin mace – Chimamanda Ngozi Adichie
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na wannan mako. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.
A wannan makon na san mai karatu zai ga darasin namu wani iri, saidai ba za ku yi mamaki ba idan muka yi duba da cewa, shafin na mata ne, don haka duk wani abu da ya shafi mata ya dace da shafin.
Darasin namu na yau zai yi duba ne kan tasirin mahaifa ga lafiyar mace, da kuma yadda ya kamata a kula da ita. Saidai ana kula da abu ne idan an san muhimmancin sa.
A duk lokacin da ake magana kan lafiyar mace, ana yawan maida hankali kan kyawunta, sheƙin fatarta ko yadda take kula da jikinta ta waje. Amma akwai wani ɓangare mai muhimmanci fiye da komai, wato lafiyar mahaifa, ma’ana sashen jikin mace da Allah Ya tanadar don ɗaukar ciki da ba da damar haihuwa. Wannan sashen, wanda a Turanci ake kira ‘uterus’, shi ne ginshiƙi ko ince tambayarin da ya bayyana mace da rawar da take takawa a duniya.
Lafiyar mahaifa ba wai kawai tana da alaƙa da iya haihuwa ba ce, har ma da tasiri mai girma a kan lafiyar ta gabaɗaya, tun daga yanayin zuciya, da ƙarfin mace wajen cimma burinta a rayuwa. Akwai cututtuka da dama da ke iya shafar mahaifa, ciki har da ‘fibroid’ (tsiron mahaifa), ciwon daji na mahaifa (cervical cancer), ko kuma matsalolin da ke samuwa bayan haihuwa, ciki kuwa har da yoyon fitsari.
A matsayin ki ta mace, kin taɓa tambayar kanki ko mahaifarki na cikin koshin lafiya?
Tambayar da wata baiwar Allah mai suna Maryam ta yi wa kanta ce shekaru bakwai da suka wuce, lokacin da ta fara lura da canjin al’adar hailarta. Ba ta ɗauki abin da muhimmanci ba har sai da ta fara zubar jini fiye da yadda aka saba, ciwon ƙugu ya addabe ta, kuma jikinta ya fara raunana. A lokacin ne ta gane akwai wani ɓangare na jikinta da ta yi sakaci da shi tsawon shekaru, wato dai mahaifa.
Mahaifa ita ce cibiyar rayuwar mace. Ita ce wajen da Allah Ya tanada domin ɗaukar ciki, kare jariri, kuma ta bayar da damar haihuwa. Amma muhimmancinta ya wuce wannan, lafiyarta tana da tasiri kai tsaye ga ƙarfin mace, yanayin jikinta, da ma farin cikinta a rayuwa.
Kamar yadda fitacciyar marubuciya Chimamanda Ngozi Adichie ta faɗa:
“Mahaifa ita ce alamar jini da numfashin mace; ita ce asalinta da ƙarfin jikinta.”
Wannan batu ba wai na likitoci kawai ba ne, batu ne da kowace mace ke buƙatar ta fahimta domin kare kanta da lafiyarta.
Mai karatu zai fi fahimtar darasin sosai idan muka fara da amsa tambayar mece ce mahaifa da kuma aikinta?
Mahaifa sashen jikin mace ne mai kama da aljihu, wanda yake a tsakiyar ƙashin ƙugu (pelvis), tsakanin mafitsara da hanji. Ita ce ke ɗaukar ƙwayar haihuwa (embryo) bayan ta haɗu da maniyyi, sannan ta ci gaba da girma har ta zama jariri.
Mahaifa tana da manyan ayyuka guda uku:
1. Haihuwa: Ita ce muhalli na ɗan adam tun daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa.
2. Tsarin haila: Mahaifa tana da rawar da take takawa a tsarin jinin haila, wanda ke nuna alamar lafiyar tsarin haihuwa.
3. Kare lafiyar mace: Matsaloli a mahaifa na iya shafar sauran sassan jiki, har ma su kawo ciwon baya, ciwon ƙugu, da matsalar rashin haihuwa.
4. Taimaka wa mace wajen ci gaba da kasancewa cikin daidaiton hormonal.
Idan wannan sashen ya lalace ko ya samu matsala, ba wai kawai tsarin haihuwa ke shan wahala ba, har ma lafiyar mace gaba ɗaya.
Idan mun fahimta, sai mu wuce ga tambayar irin matsalolin da ke iya shafar mahaifa:
1. Fibroid: Wannan ƙurji ne ko na ce tsiro da ke fita a mahaifa har ya kai ya girma, saidai kuma mara cutar da kansa ne, saidai yana iya jawo:
Zubar jini da yawa yayin haila, ciwon ƙugu, matsalar samun ciki. Kuma yana ɗaya daga cikin alamomin wannan tsiro, wasa da al’ada zata dinga yi, ko kuma ya bayyanar da alamomin ciki, amma ba cikin ba ne. Idan ma ya riƙa, har motsi yake yi irin na juna biyu.
Dakta Halima Yusuf, likitar mata a Asibitin Koyarwa na ABU Zaria, ta bayyana cewa: “Mafi yawan mata masu fibroid ba sa sanin suna da shi sai lokacin da matsaloli suka fara. Gwajin lafiya akai-akai shi ne kawai mafita.”
2. Kansar mahaifa (Cervical Cancer): Tana samuwa ne sakamakon kamuwa da kwayar cutar HPV ko wasu dalilai na rayuwa. ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke kashe mata a duniya, sau da yawa yana faruwa sakamakon kamuwa da ƙwayar cutar HPV.
Rigakafinsa ya haɗa da yin Pap smear, gwajin HPV, da allurar rigakafi tun kafin mace ta fara kwanciyar aure. Alamunsa sun haɗa da; zubar jini bayan saduwa ko bayan haila, ciwon ƙugu mai tsanani.
3. Matsalolin bayan haihuwa: Wasu mata kan fuskanci raunin mahaifa bayan haihuwa, wanda zai iya kawo matsalolin rashin tsayayyen fitsari, ko matsalar saukar mahaifa (prolapse). Da wasu cututtuka na daban.
Alamunsa sun haɗa da; matsalar riƙe fitsari, jin nauyi a ƙugu, wahalar yin ayyukan yau da kullum.
Darajar lafiya da haihuwa a al’adar Hausa:
Hausawa tun da daɗe suna ganin uwa a matsayin ginshiƙin iyali. Kamar yadda masu azancin zance suke cewa, “Uwa ta fi gata, domin ita ke ba da rai.”
A gargajiyance, ana ganin mace da ta samu matsala a haihuwa ko hailarta a matsayin mai buƙatar kulawa ta musamman. Don haka zamanin na da, ana kai ta wajen dattijo ko mace mai ilimin gargajiya. A da ma kenan an yi hakan, ina ga yanzu da komai ya zo da sauƙi, sakamakon ci gaban kimiyya ya kawo hanyoyin rigakafi da magani da suka fi saurin ba da mafita.
An jima ana yekuwa tare da faɗakar da mata kan muhimancin kula da mahaifa, hakan ya sa za a iya samun tarin maganganu daga ƙwararru da shahararrun mutane game da mahaifa, a ƙoƙarin da suke na wayar da kan al’umma musamman mata.
Dakta Hadiza Balarabe, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, ta taɓa faɗar cewa, “Babu wata mace da za ta iya ba da cikakkiyar gudunmawa ga iyali da al’umma idan lafiyarta ta jikinta ba ta da inganci. Kula da mahaifa kula ce ga rayuwar gaba ɗaya.”
Shahararriyar jaruma, kuma mai gabatar da shirin talabijin Oprah Winfrey, ta taɓa kira ga mata kan muhimancin lafiyarsu, inda take cewa,“Jikinki shi ne kayan aikinki; ki kula da shi kamar yadda kike kula da rayuwarki.”
Shawarwari don kula da lafiyar mahaifa:
1. Yin gwaje-gwaje akai-akai: Gwajin Pap smear don gano cutar mahaifa da wuri. Gwajin HPV.
2. Abinci mai gina jiki: Cin kayan marmari, kayan lambu, da abinci mai ƙarancin mai.
3. Hutawa tsakanin haihuwa: Bai wa mahaifa damar murmurewa.
4. Rigakafin Cutar HPV. Allurar rigakafin HPV ga ‘yan mata tun suna ƙanana ko kafin su yi aure.
5. Kula da nauyin jiki. Rashin ƙiba yana rage haɗarin cututtuka da dama.
6. Gujewa shan taba da barasa: Suna ƙara haɗarin cututtuka.
7. Motsa jiki: Hakan yana ƙarfafa ƙashin ƙugu.
8. Tuntuɓar likita da zarar an ga alamar matsala.
ƙididdiga mai faɗakarwa:
Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO, ta ƙiyasta cewa, kowace shekara, fiye da mata dubu ɗari uku a duniya na mutuwa sakamakon cutar kansar mahaifa. Kimanin mata miliyan 20 a Afirka na fama da fibroid. Fiye da rabin waɗannan mutanen ba su san suna da matsalar ba saboda rashin yin gwaji da wuri.
Daga ƙarshe muna kira da a lura da cewa, mahaifa ita ce cibiyar rayuwar mace, tushen ƙarfinta, da muhallin asalin jikinta. Kula da lafiyar mahaifa ba kawai kariya ce daga cututtuka ba, har ma tabbatar da cewa, mace za ta iya taka rawarta a cikin iyali da al’umma cikin koshin lafiya da farin ciki.
Kamar yadda Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta taɓa faɗa: “Idan mace ta kula da jikinta, tana kula da makomar ƙasarta.”
Saboda haka, ya kamata kowacce mace ta sanya kula da lafiyar mahaifa cikin jerin abubuwan da ba ta wasa da su a rayuwarta. Wannan jari ne da zai dawo mata da riba har tsawon rayuwarta.
