Blueprint ta ƙarfafa alaƙar aiki da kamfanin dillancin labaran ƙasar Sin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Chana kan harkokin aikin jarida, tawagar kamfanin dillancin labarai na Xinhua daga hedikwatarsa na Afrika ta ziyarci babban ofishin jaridar Blueprint da ke Abuja.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Mista Huang Wei, wato mataimakin editan Xinhua a Afirka, ta kuma kunshi Mista Nie Zuguo, Shugaba a Kampala; Mr. Zhou Nan, Manajan kasuwanci a Afirka; da Mista Yang Zhe, shugaba reshensa na Nijeriya.

Huang Wei ya yaba wa Blueprint bisa ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da kamfanin ta fuskar ƙwarewa a harkar aikin jarida, yana mai kira da a faɗaɗa hanyoyin haɗaka don inganta ƙawance tsakanin Nijeriya da Sin.

Ya kuma bayyana muradin kamfaninsu na haɗa hannu da Blueprint musamman a Nijeriya tare da ƙoƙarin ɗorewa akan haka.

Da ya ke jawabi yayin yi wa baƙin maraba, Darakta Manaja na jaridar Blueprint, Alhaji Salisu Umar, ya bayyana alaƙar ɓangarorin biyu a matsayin abinda ake kira da “tsintsiya maɗaurinki ɗaya”, yan mai tabbatar da buƙatar haɗin-gwiwar.

Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa, Blueprint za ta bada gagarumar gudunmuwa wajen yaɗa manufofin Xinhua a jaridunta da ake bugawa kullum da kuma sashenta na yanar gizo ciki har da batutuwan ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Chana.

By Babaji