Hukumar NCC ta horar da mata 100 sana’o’in zamani a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta horar da mata 100 sana’o’in fasahar zamani domin ƙarfafa musu gwiwa su zama masu dogaro da kai.

Shugabar Sashen fasahar dijital na hukumar, Hajiya Hauwa Wakil a jawabinta a wajen ƙaddamar da horon da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Talata, ta yi kira ga mata da su ba da fifiko kan sana’o’in kasuwanci na zamani domin ci gaban su.

Ta ce, an zaɓo mahalarta taron ne daga dukkan ƙananan hukumomi 14 na Zamfara domin su ci gajiyar shirin.

A cewarta, hukumar a shirye take a koda yaushe don tallafa wa mata da kuma bai wa mata damar sanin ilimin zamani kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan ta hanyar fasahar zamani.

Hajiya Hauwa ta kuma ƙalubalanci mata da su rungumi amfani da fasahar zamanin kasuwanci, inda ta bayyana cewa, ƙasa da kashi 20 cikin 100 na matan Najeriya suke amfani da fasahar zamani watau dijital skills a turance.

“Wannan shi ne juyin juya halin masana’antu na huɗu kuma ba zai jira kowa ba, dole ne ku shiga cikin tsarin ko kuma a bar ku a baya, za a ƙarfafa ku da kuma samar muku da fasahar dijital da ake buƙata”. Hauwa tace.

A nasa jawabin Sakataren zartarwa na hukumar sadarwa ta Najeriya Dr. Aminu Maida wanda Malan Abubakar Kurfi ya wakilta mai kula da shiyyar Kano ya ce, babban burin hukumar shi ne ƙarfafawa mata da sarrafa nau’o’in sana’o’in hannu domin samun ci gaban tattalin arziki na zamani.

A jawabin maraba, sakataren zartaswa na hukumar fasaha da ci gaba ta Jihar Zamfara (ZITDA), Habibu Gajam ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na cimma muhimman fannoni guda huɗu na ayyukan tattalin arziki na zamani da nufin ƙarfafawa mata gwiwa.

Ya kuma yabawa hukumar NCC bisa horar da matan Zamfara kan sana’o’in zamani, inda ya ƙara da cewa akwai sauran abubuwan da ke tafe akan hanyoyin sadarwa na 4G da 5G.

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, wanda mataimakin gwamna Malam Mummuni ya wakilta ya yi alƙawarin tallafawa shirin NCC na bunƙasa ayyukan fasahar zamani a jihar.

“Zamu tabbatar da ganin an samu ɗorewar shirin domin hukumar NCC za ta bi diddigin nasarorin da aka samu. Mataimakin gwamnan ya ce.

Idan za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Yuni, 2025 Jihar Zamfara ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta ƙaddamar da tsarin fasahar zamani ta fannin karatun zamani.

Wakilin mu ya tattaro cewa, bayan kwashe kwanaki huɗu ana wannan horon, hukumar ta NCC ta sashenta na tattalin arziki na dijital za ta sake gudanar da wani horo kan dabarun horas da mata na dijital, kowanne daga cikin mahalarta 100 za a basu wayoyin hannu yayin da gwamnatin jihar ta yi alƙawarin bayar da naira dubu dari a matsayin alawus-alawus ga waɗanda aka horar.

By ukarofi