Majalisar dokokin Katsina ta amince da kafa hukumar samar da lantarki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dokar ta samu amincewar majalisar ne bayan gabatar da rahoton kwamitin ayyukan cigaba da walwalar al’umma, ƙarƙashin jagorancin Hon. Mustapha Tukur Ruma, inda Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai, ya karanta dokar na uku kuma na ƙarshe domin tabbatar da ita.

Hon. Dabai, yace kafa hukumar zai inganta samar da hasken wutar lantarki cikin sauƙi ga al’umma ta hanyar amfani da ingantattun kayan aiki na zamani.

Bayan amincewa da dokar, kakakin majalisar ya umarci akawun majalisa da ya tura cikakken kwafin ta ga gwamnan jihar domin sanya hannu.

Haka kuma ɗan majalisa mai wakilan karamar hukumar Ƙafur ya kawo ƙudiri a zauren majalisar na neman gwamnatin jihar Katsina ta gyara hanyoyin samar da wutan lantarki a ƙauyukan Malumfashi zuwa Ƙafur.

Ƙauyukan sun haɗa da Malumfashi zuwa Yartalata, Tagwayen Marke,Dantutture,Dankanjiba,

A zaman na ranar Talata, majalisar ta kuma amince da gyare-gyare ga sashe na bakwai, takwas, da 14, gami da tsari na biyu na dokar kafa hukumar kula da ma’aikatan majalisar dokoki (Doka ta Biyar, 2018). Amincewar ta biyo bayan rahoton kwamiti na musamman ƙarƙashin jagorancin Hon. Umar Ali Bindawa.

Haka zalika, majalisar ta amince da ƙudurin da Hon. Sha’aibu Wakili, mai wakiltar Ƙafur, ya gabatar na buƙatar gyara hanyoyin samar da wutar lantarki daga Malumfashi zuwa Yartalata, Tagwayen Marke, Dantutture, Dankanjiba, Kurmi, Nasarawa, da Gamzago, duk a ƙaramar hukumar ƙafur. Bayan tattaunawa da amincewa, kakakin majalisar ya umarci akawun majalisa da ya tura wannan ƙuduri zuwa ɓangaren zartarwa domin ɗaukar mataki na gaba.

Majalisar ta amince da ƙudirin inda kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya umurce akawun majilisar ya turawa gwamnatin domin tayi abinda ya dace.

By ukarofi