Ambaliyar Neja: Tinubu ya amince da biliyan N16.7 don sake gina gadar Mokwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da ke jihar Neja da ambaliya ta lalata a watan Mayu, 2025.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ya faɗi hakan a yau Asabar bayan ganawa da Ministan Ayyuka Dave Umahi a Abakaliki, babban birnin jihar Ibonyi.

Umahi a nasa jawabin ya ce shugaban ƙasar ya amince da yin irin aikin a jihohi da dama na faɗin ƙasar.

Umahi ya bayyana cewa, sauran gadajen da za a yi aikinsu sun haɗa da gadar Wukari a jihar Taraba, da ta Lokoja a jihar Kogi, da ta Afikpo a Ebonyi, da gadar sama ta Keffi a Nasarawa.

Sai kuma da gadar Jebba a Kwara, da gadaje bakwai a Edo, da kuma wata a Kebbi.

Kimanin mutane 150 suka rasa rayukansu yayin ambaliyar Ƙaramar Hukumar Mokwa wadda ta lalata gidaje da ɗaiɗaita dubunnan mutane a watan Mayu.

By Babaji