Jagororin Ansaru da suka kitsa fashin magarƙamar Kuje a 2022 sun shiga hannu, inji Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ta’addanci a Nijeriya, rundunar sojoji ta yi nasarar kama manyan ƴan ta’addar ƙungiyar Ansaru biyu, wato Abu Baraa da Mahmuda.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro NSA, Nuhu Ribaɗu ya bayyana haka a yau Asabar yayin ganawa da manema labarai a cibiyar kula da ayyukan daƙile ta’addanci (NCTC) da ke Abuja.

Ribaɗu ya ce, an kama sanannun kwamandojin ne yayin atisaye da dama da dakarun tsaron suka gudanar tun daga watan Mayu, 2025.

Ya ce, kwamandoji biyun suna daga cikin waɗanda ake nema ruwa-a-jallo na tsawon shekaru duba da cewa suna da hannu a fasa gidan gyaran hali na Kuje da aka yi a 2022, lamarin da ya yi sanadin tserewar fursunoni 900 ciki har ƴan ta’adda da aka yanke wa hukuncin kisa.

Baya ga haka, ƴan ta’addar suna da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya inda suka riƙa harin sanannun ƴan ƙasa, jami’an gwamnati da matafiya a manyan tituna.

By Babaji