Zaɓen cike gurbi: ‘Yan sanda a Kano sun cafke matasa 200 masu neman tada tarzoma

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Fiye da matasa 200 ne suka faɗa komar jami’an tsaro a yayin zaɓen maye gurbi a ƙaramar hukumar Shanono-Bagwai da Ghari-Tsanyawa.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar ta Kano Ibrahim Bakori ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Kano a ranar Asabar.

A saƙon da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan reshen jihar ta Kano SP Abdullahi Kiyawa ya aika wa manema labarai yace matasan da aka kama bisa yunƙurin kawo tarzoma a yayin zaɓukan sun kai 288 an kuma kama su da makamai kala-kala da suka haɗar da bindigogi da adda da kwari da baka da sauransu.

Matasan da ake zargin masu tada zaune tsaye ne sun faɗa komar jami’an tsaron bayan da aka kama su da makamai, wasunsu kuma da ƙoƙarin tada zaune tsaye yayin zaɓukan na maye gurbin ƴan majalisar jiha na ƙananan hukumomin na Shanono-Bagwai da kammala zaɓen na Ghari-Tsanyawa.

By ukarofi