Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano ta yi godiya ta musamman ga Sheikh Nuhu Idris Fallata, bisa tallafin kayan aikin tsaro da ya bayar ga kwamitin bijilanti na jiha.
Taron miƙa tallafin da ya gudana a Officers Mess da ke Bompai Kano, ranar Alhamis.
Tunda farko a jawabinsa, wakilin Sheikh Nuhu Idris Fallata, Ambasada Aliyu Lawan Saulawa, ya miƙa kayan tallafin ga kwamishinan ƴan sanda na Kano, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma wajen magance matsalolin tsaro, musamman ma ganin yadda lamarin ke ƙara ta’azzara a birnin Kano.
Ambasada Saulawa ya bayyana cewa kayan da aka bayar sun haɗa da: Gorori guda 1000, fitilun cocila guda 500, batiran sola huɗu, fanal huɗu, Inbata huɗu, da usur guda 1,000 da kuma rugunan ruwa guda 200.
Ya ƙara da cewa, “Wannan tallafi da Fallati ya bayar ba wai yau ya fara ba, yau ya baiwa ƴan bijilanti, insha Allah kafin wata ɗaya akwai na ƴan sanda da za’a ba a su duka, abin ana yi ne domin a tallafawa ita kanta gwamnatin Kano da kuma al’ummar Kano” inji Ambasada Aliyu
A nasa jawabin, kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, wanda DCP Lawan Mani ya wakilta, ya nuna godiyarsa ga Sheikh Nuhu Idris Fallata da ƙungiyarsa kan wannan gudunmawa mai muhimmanci wajen ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.
DCP Lawan Mani ya ja hankalin kwamitin bijilanti da su kiyaye dokoki a yayin gudanar da ayyukansu, tare da shawartar su riƙa sanar da ofishin ƴan sanda mafi kusa kafin su fita aiki da bayan dawowarsu domin inganta haɗin kai da samun nasarar aiki.
Shugaban kwamitin bijilanti na Kano, Shehu Muhammad Rabiu, ya bayyana godiyarsa ga Sheikh Nuhu Idris Fallata kan wannan taimako, tare da tabbatar da amfani da kayan yadda ya dace domin bunƙasa tsaro a jihar.
