Mu ƙarfafawa ’ya’ya mata gwiwa kan neman ilimi

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na cika da murna da farin ciki, sakamakon samun labarin nasarar da wasu ’yan mata uku ’yan Nijeriya suka samu a gasar gwada gwanintar Turanci da muhawara da aka gudanar a birnin Landan, ƙarƙashin wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta TeenEagle Global. ƙasashen duniya 69 ne suka samu halartar wannan babbar gasa ta matasa ’yan ƙasa da shekara 20.

Nafisa Abdullahi Aminu, Rukayya Muhammad Fema, da Hadiza Kalli Kashim su ne ‘yan matan da suka samu nasara a wannan gasa. Kuma wani ƙarin abin burgewa shi ne kasancewar su ’yan Nijeriya daga Jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabas. Wannan nasara ta su abin alfahari ce ga duk wani ɗan Arewacin Nijeriya, musamman kasancewar gasar ba ta ƙasashen Musulmi ba ce ko ta addini ba. Gasa ce akan harshen Turanci, harshen da ake amfani da shi a harkokin gwamnati da koyar da ilimin boko. Kuma kasancewar waɗannan yara sun fito daga yankin da ake yi wa kallon shi ne koma baya ga ilimin boko, da ƙarancin bai wa ’ya’ya mata goyon baya su yi ilimi. Sannan uwa-uba, yankin da ya ƙyanƙyashe ƙungiyar ’yan ta’addan Boko Haram, da ke yaƙi da aƙidojin boko da sanya yara mata a makarantun da ba na addini ba.

Ba tun yanzu ba, yankin Arewa na shan suka da shaguɓe daga ’yan kudu, saboda kallon da ake yi mana a matsayin waɗanda ba su waye ba, kuma ba su da kyakkyawan tsarin ilimin zamani, kamar yadda a kudu ake alfahari da shi, kuma suke cin gajiyar sa. Al’adar mu ta yi wa yara mata aure da wuri, ya sa ake mana kallon masu tauye haƙƙoƙin yara mata da hana su damar yin karatu mai zurfi, da ƙuntatawa rayuwar su a ƙarƙashin farfajiyar aure da addini. Alhalin yawanci masu faɗar haka ba su taɓa zama a Arewa ba ko kuma ziyartar makarantun mu su ga yadda yara mata suka ninka maza a ajujuwa, kuma suke yin zarra a karatu. Yayin da a wasu jihohin Arewa ma ilimi ya zama kyauta, musamman ga mata. Sai dai suna samun bayanan su ne daga tsofaffin rubuce-rubuce da wasu maƙiya cigaban Arewa suka rubuta, don dakushe ci gaban da muke samu.

Ba ina nufin in ƙaryata cewa, a Arewa akwai ƙalubalen sa yara mata a makarantun boko ba ne, ko kuma nuna halin ko-in-kula da iyaye da gwamnatoci ke nunawa game da ilimin mata ba ne. Amma ina ƙoƙarin in nuna cewa, wannan tsohon labari ne wanda ya daɗe da wucewa. Yanzu Arewa ta farka, ilimin zamani da na addini sun zama fitilun da suke haska kowanne gida, komai talaucin sun. Lallai, muna sane da muhimmancin da addini ya nuna mana game da ilimantar da ’ya’ya mata, a matsayin su na iyayen al’umma.

Su Nafisa mai shekaru 17 da Ruƙayya mai shekaru 15 sun isa su zama misali ga gwagwarmayar da iyaye da malamai ke yi na samar da ingantaccen ilimi ga maza da mata. Bincike ya tabbatar da cewa, waɗannan ’yan mata ɗalibai ne a makarantar Tulip International College (NTIC) da ke garin Potiskum a Jihar Yobe, wacce makaranta ce mallakin ƙasar Turkiyya. Wacce makaranta ce ta yaran masu hannu da Shuni da ke ba da kyakkyawar kulawa da ingantaccen tsarin koyarwa ga ɗaliban su.

Duk da kasancewar makaranta ce ta mai zaman kanta, ba ta gwamnati ba, amma kasancewar ta a Arewa, kuma ɗaliban ‘ya’yan mu ne, shi ma abin da za mu yi alfahari da shi ne. Na ji har Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kansa ya jinjina musu, tare da yabawa Gwamnatin Jihar Yobe bisa gudunmawar da take bai wa harkar ilimi. Kodayake wannan ba nasara ce ta gwamnati ba, ƙoƙari na malamai da iyayen waɗannan yara, da suka himmatu don ganin sun nuna wa duniya bajintarsu, da ƙoƙarin da Nijeriya ta Arewa ke yi na ganin ta yi gogayya da kowacce ƙasa ta duniya a fannin ilimi.

Amma duk da haka, nasarar su tamu ce baki ɗaya, ba ga gwamnati da jama’ar Jihar Yobe ko makarantar Tulip International College kaɗai ba, waɗanda wannan nasara ta zama musu ƙarin dama ta samun ɗalibai, har da dukkan wani ɗan Arewa. Sannan harwayau ƙalubale ne ga shugabannin mu na Arewa, musamman gwamnatocinmu da masu hannu da shuni su ƙara dagewa wajen farfaɗo da darajar ilimi, da inganta makarantun gwamnati da aka yi watsi da su. Abin kunya ne yadda gwamnati ta yi sakaci makarantun gwamnati suka lalace, aka bar wa ’ya’yan talakawa da marasa gata, yayin da masu kuɗi da jami’an gwamnati ke kai ’ya’yansu manyan makarantu masu tsada a ciki da wajen ƙasar nan, suna samun ilimi mai inganci.

Babu wani abu da ya zarce ilimi daraja da kawo wa rayuwar ɗan adam cigaba, kamar ilimi. Kuma matuƙar muna so Arewa ta samu ci gaban da take so, kuma ta yi kima da daraja a idon duniya, dole ne sai mun tashi da gaske mun gyara makarantun mu na gwamnati. Ba irin gyaran gini da kwaskwarima da wasu ’yan siyasa ke yi ba, wanda za ka ga an yi wa aji ɗaya ko biyu fenti, ana yaɗawa a zaurukan sada zumunta cewa, wane ya ceto ilimi ko yaran talakawa na samun moriyar dimukraɗiyya. Bayan gyaran gini, a samar da kujerun zama na zamani, a ɗauki ƙarin malamai masu takardun NCE waɗanda suka goge a harkar koyarwa. A basu horo na musamman, don su samu dabarun koyarwa na zamani da zai dace da kowacce makaranta ta duniya. A inganta albashin malamai, su daina zama almajirai, a ƙara musu ƙwarin gwiwa, don su ƙara sadaukarwa da nuna jajircewa wajen koyarwa.

Na karanta a wani waje cewa tsohon Ministan Sadarwa, kuma babban malamin Sunnah a Nijeriya, Sheikh Isa Ali Pantami, ya buƙaci shugaban ƙasa da ta bai wa waɗannan ɗalibai kyautar manyan kuɗaɗe da shaidar karramawa ta ƙasa ta OON, kamar yadda aka yi wa ’yan ƙwallon ƙafa na mata da suka ci nasarar cin kofin ƙasashen Afirka na mata a kwanan nan. Wannan abin a yaba ne shi ma, idan har gwamnati za ta yi hakan, domin zai ƙara nunawa duniya cewa Nijeriya tana girmama ilimi sosai.

Muna fatan ubangiji Allah Ya ƙara yawaita mana irin waɗannan yara, kuma Allah Ya albarkaci karatunsu, Ya ba su kyakkyawar rayuwa da ɗaukaka a dalilin wannan nasara da suka samu.

By ukarofi