Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ƙungiyar Tattaunawa Don Kawo Mafita da Maslaha ta Fulani (FDF), reshen jihar Filato, ta bada shawara don samun zaman lafiya a jihar.
A cikin sanarwar da ta fitar a ƙarshen taron da aka yi a ranar Asabar, ƙungiyar ta ce a shirye ta ke ta ba da damar zaman lafiya idan har gwamnati da ‘yan jihar suka cika sharuɗɗan ta.
Sanarwar wacce shugaban FDF, Alhaji Shehu Buba da Sakatare Salihu Musa Umar suka sanya wa hannu, mai taken ‘Buɗaɗɗiyar Matsayin Al’ummar Fulani a Jihar Filato, ta ƙunshi sharuɗɗan da suka haɗa da samar da ayyukan yi ga matasan Fulani, da yin adalci ga makiyayan da suka rasa shanunsu, da ’yancin yin kiwo a hanyoyin da aka tanada da kuma fitar wa Fulani rabon su a cikin arzikin jihar yadda ya kamata.
Sassan sanarwar sun ce: “Domin zaman lafiya ya dawo jihar Filato, al’ummar Fulani na buƙatar a cika waɗannan sharuɗɗa:
“Za a ba mu aikin yi kamar yadda ake ba ’yan ƙabilar Berom. A kodayaushe ’yan ƙabilar Berom su na daƙile duk wani yunƙuri da muke yi na ganin mun yi aiki a ma’aikatun gwamnati wanda hakan ke saka mu zama baƙi a filayenmu na gado kaka da kakanni.
“Gwamnatin Jihar Filato ta yi mana rashin adalci wajen rabon arzikin jihar, muna roƙon gwamnatin Jihar Filato da ta yi mana adalci wajen ganin ta mutunta haƙƙinmu a matsayinmu na ‘yan ƙasa na gaskiya ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, ta kuma samar mana da ayyukan ci gaba kamar asibitoci, hanyoyi, ruwan sha, wutar lantarki da sauransu.
“Haka kuma, ‘yan ƙabilar Berom tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Filato da ‘yan sanda sun hana mu ’yancin gudanar da harkokin kasuwanci da noma, su na yin hakan ne ta hanyar kwace mana filayen noman ta hanyar kai hare-hare tare da lalata dukiyoyinmu, dole ne a kawo ƙarshen su idan har ana son a samu zaman lafiya.
“Muna sane da cewa duk hanyoyin kiwo da hannun jari an kafa su ne kuma doka ta ba su goyon baya a shekarar 1965, ciki har da Jihar Filato, amma a yau a ƙananan hukumomin Wase, Jos ta Kudu, Jos ta Arewa, Bokkos, Mangu, Riyom, Barkin Ladi da Bassa, kashi 60 na wuraren kiwo da hanyoyin hannun jarinmu ko dai gonaki ne ko na gida, kuma gwamnati ta ƙi yin wani abu a kai,” inji sanarwar
“’Yan asalin Filato sun yi wa al’ummarmu barna da kuma abubuwan da suka shafi al’ummar Jihar Filato tun daga shekarar 2010 zuwa yau, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da ’yan ƙabilar Berom suka yi mana ya fi tayar da hankali, da ban tsoro, da tashin hankali.
“Saboda haka yana da matuƙar amfani mu bayyana da kuma bayyana wasu daga cikin wazannan abubuwan da suka faru marasa daɗi da kuma munanan illolin da suke yi ga jama’armu ta yadda duk wanda ya damu da tattaunawa da mu domin samun zaman lafiya ya fahimci irin ƙorafe-ƙorafen da muke yi kan al’ummar Berom.
“A shekarar 2010 da kuma shekaru masu zuwa, ‘yan ƙabilar Berom tare da goyon bayan gwamnatin jihar da majalisar gargajiya ta Berom, sun kai mana hari a wurare daban-daban ba tare da wani tsokana ko kaɗan ba, sun kashe mu ba tare da jinƙai ba, sun sace mana shanu da yawa, sun ƙona gidajenmu, sun kore mu da ƙarfi daga filayen da muka mallaka.
“An kashe mu ɗaruruwa maza da mata da ƙananan yara tare da raunata wasu da dama, an kashe ko kuma an sace mana shanu da dama, an raba dubban mutane da muhallansu, an lalata mana gidajenmu.
