Zamfara: INEC ta ayyana zaɓen majalisar dokokin Ƙaura Namoda bai kammala ba

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen majalisar dokokin jihar da aka gudanar a mazabar Ƙaura Namoda ta Kudu a matsayin wanda bai kammala ba.

Jami’ai biyu da suka gudanar da zaɓen, Dakta Sa’ad Lawal da Dr. Aminu Idris ne suka sanar da hakan.

A cewarsu, za a gudanar da kammala zaɓen a runfunan zaɓe biyar na Kyambarawa da Sakajiki.

Sun kuma bayyana cewa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC za ta sanar da wata rana na kammala zaɓen da ba a kammala ba.

Blueprint ta tattaro cewa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar tana da kuri’u 5,341 yayin da jam’iyyar All Progressive Congress APC ke da ƙuri’u 7001.

Hakazalika jam’iyyar APC ce ke kan gaba da ƙuri’u 1,660.

By ukarofi