Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
9Mobile, Kamfanin Sadarwa na huɗu mafi girma a Nijeriya, ya rikiɗe zuwa T2 ranar Juma’a, cikin ingantaccen tafarki wanda ya nuna wani sabon zamani a masana’antar sadarwar Nijeriya.
Sake sunan ya haɗa da ƙwaƙƙwaran canji daga kalarsa ta kore zuwa launin lemu.
An ruwaito cewa, wannan gagarumin sauyi ne a fannin sahihancinsa da dabarunsa, matakin da ya buɗe wani sabon babi ga kamfanin a yayin da ya ke ƙoƙarin sake fayyace rawar da zai taka a kasuwar sadarwa ta Nijeriya.
Sake sunan, a cewar babban jami’in gudanarwar kamfanin Obafemi Banigbe a wajen taron ƙaddamarwa, mai taken “Tech Meets Ten” canji ne babban ya wuce kwaskwarima.
Banigbe ya bayyana canjin a matsayin dabarar sake fasali da nufin sanya sunan T2 a matsayin alamar abokin ciniki.
Ya jaddada cewa T2 za ta mayar da hankali ne wajen ƙarfafawa ‘yan Nijeriya a sassa daban-daban, tun daga masu kirkiro da ma’aikata masu nisa zuwa masu farawa da masu amfani da yau da kullum, ta hanyar samar da wata hanyar da za ta bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da haɗin kai.
Sake suna ya zo ne shekara guda bayan da LH Telecommunication Limited ya samu kashi 95.5 na hannun jarin 9mobile, wanda ke nuna sabon tsarin mallaka.
Kamfanin, wanda a baya yana aiki a matsayin Etisalat kafin ya mayar da sunan 9mobile a shekarar 2017, ya fuskanci ƙalubale a shekarun baya.
