Nijeriya na asarar ɗimbin albarkatun ƙasa sanadin tashin gobara – Masani

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Manajan Darakta na Hoist Life Safety System Limited, Adeleye Oladimeji, ya bayyana damuwarsa kan ɗimbin albarkatun da Nijeriya ke asara duk shekara saboda yawan tashin gobara da ke afkuwa a faɗin ƙasar.

Oladimeji ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce, jihar Legas kaɗai ta yi asarar kadarorin da suka kai kimanin Naira tiriliyan 1 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, ban da adadin mutanen da aka yi asarar a lokacin.

“A cikin wata yarjejeniya da masu ruwa da tsaki da muka yi a baya-bayan nan, an ba da rahoton cewa mutane 218 ne suka mutu sakamakon aukuwar tashewar tankar mai a cikin wannan shekarar (2025) kaɗai,” inji shi.

Manajan daraktan, wanda injiniya ne, ya bayyana farin cikinsa yadda masu manyan motoci ke nuna sha’awar wannan shiri na inganta ayyukan kashe gobara ta hanyar haɗin gwiwa.

Ya ƙarfafa ‘yan Nijeriya da su ƙara nuna sha’awar zaukar matakan daƙiile ɓarkewar gobara, fiye da garzaya zuwa ga gwamnatin tarayya domin a kula da lafiyarsu bayan iftila’in ta afku.

“Lokacin da kuka ci gaba da yin asarar dukiyoyi kuma abin da ku ke yi shi ne sake ginawa, ba za ku iya samun ci gaba a matsayinku na ’yan kasuwa ba.

“Ya kamata ƙasar nan ta samu ci gaba ba mataki ɗaya a gaba da koma baya ba saboda ɓarkewar gobara.

“A cikin wannan shekarar, wata kasuwa a jihar Kano ta yi asarar shaguna kusan 500 a sanadiyyar gobara, haka ma ta faru a jihar Sokoto, da kasuwannin Maiduguri, da Mandalas da kuma kasuwannin Dosumu, duk a jihar Legas,” inji shi.

A cewar Oladimeji, ɗaukar matakan da suka dace shi ne kan gaba.

Dangane da shirin ɗaukar ƙarin ma’aikata a hukumar kashe gobara ta tarayya, ya ce matakin zai ƙara haɓaka haɗin gwiwa tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar gobara a ƙasar nan.

“Mun kammala horar da ma’aikatan hukumar kashe gobara 2,500, tare da ɗaukar ƙarin ma’aikata 4,000, za a samu ma’aikatan da ake buƙata don yaƙi da kashe gobara a hankali a hankali,” inji shi.

Oladimeji, ya ce har yanzu ana buƙatar ƙarin kulawa a fannin samar da ababen more rayuwa.

Ya bayyana cewa kamfanoni da yawa su na da kayan kashe gobara amma su na ajiye ba a aiki da su saboda rashin ma’aikatan da suka dace.

By ukarofi