Matatar Dangote ta fitar da tankokin CNG 4,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar Mai ta Dangote ta sanar da fitar da iskar gas ɗin da ake kira ‘Compressed Natural Gas’ (CNG) guda 4,000. 

Fitar da tankokin wani ɓangare ne na babban shiri na sauya fasalin mai a Nijeriya.

Tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025, matatar za ta fara isar da man fetur da dizal kai tsaye zuwa gidajen mai, masana’antu, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu saye – ba tare da wasu cajin kuɗaɗe ba.

A cewar matatar, ana sa ran shirin zai ceto ‘yan Nijeriya daga kashe sama da tiriliyan N1.7 a duk shekara, da rage farashin mai, da samar da ayyukan yi sama da 15,000, da kuma farfaɗo da gidajen man da ke kwance a faɗin ƙasar nan. 

Haka nan ana hasashen amfani da manyan motocin da suke amfani da gas na CNG zai rage hayaƙi mai guba sosai tare da samar da mafi tsafta kuma mai ɗorewa madadin amfanin da man dizal wajen jigila.

Shirin wani ɓangare ne na saka hannun jari na biliyan N720, wanda ya haɗa da tsare-tsaren kafa cibiyar sadarwa ta tashoshin CNG a faɗin ƙasar. Wannan zai tabbatar da ci gaba da wadata tare da inganta samar da makamashi don sama da ƙananan masana’antu da matsakaitan masana’antu (MSME) miliyan 42.

Yayin da take bayyana ci gaban a matsayin “sabon zamani a cikin araha, abin dogaro, kuma mai ɗorewa,” matatar Dangote ta ce aikin zai inganta ci gaban tattalin arziki da ɗorewar muhalli.

By ukarofi