Nijeriya za ta mayar wa Amurka martani game da sabuwar dokar biza

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon tsarin neman bizar Amurka ya jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya bayan da hukumomi suka kawo sababbin dokoki.

Amurka ta ce dole ne masu neman biza daga Nijeriya su bayyana dukkan bayanan kafofin sada zumunta da suka yi amfani da su a tsawon shekara biyar da suka gabata.

A saƙon da ta wallafa a shafin ɗ, Amurka ta ce matakin na cikin tsarin tantance mutane da sahihancin bayanan masu neman bizar.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ba za ta yi shiru game da wannan doka ba, domin za ta ɗauki irin matakin ga duk wani ɗan ƙasar Amurka da ke neman biza a Nijeriya.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana wannan a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta riga ta samu sanarwa daga Amurka kafin aiwatar da matakin.

Amurka ta ce daga yanzu duk wanda ke neman bizar ƙasar dole ne ya cike fom na DS-160 tare da lissafa dukkan asusun kafofin sada zumunta da ya taɓa amfani da su a tsawon shekara biyar.

An ce duk wanda ya boye bayanan zai iya fuskantar ƙin amincewa da neman bizarsa, tare da rasa damar sake neman biza nan gaba.

Hukumomin Amurka sun yi gargadin cewa yana da muhimmanci masu neman biza su fadi bayanai na gaskiya.

Wannan ya sa suka jaddada cewa duk wani ɓoye bayani ko karya na iya zama babban ƙalubale ga mai neman biza.

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin daidai da abin da Amurka ta yi.

Ebienfa ya bayyana cewa duk ɗan ƙasar Amurka da ke neman biza a Nijeriya zai fuskanci irin dokar.

Ya ce zai zama wajibi a bayyana dukkan bayanan kafofin sada zumunta na shekara biyar.

Ya ce gwamnati za ta gudanar da taro tsakanin hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Cikin Gida da kuma Hukumar Tsaro ta NIA.

Ebienfa ya bayyana cewa tattaunawar za ta kasance ne domin tabbatar da cewa matakin da Najeriya za ta ɗauka ya yi daidai da bukatun tsaro da tsarin diflomasiyya.

Ya ce taron zai tabbatar da cewa dukkan hukumomin da abin ya shafa sun amince da tsarin aiki guda ɗaya.

By ukarofi