Gwamnan Kano ya rantsar da sabon Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da mashawarta uku

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da magance cin hanci da rashawa na Jihar Kano Alhaji Sa’idu Yahaya. 

Haka kuma Gwamna ya samu damar damar rantsar da tsohon Shugaban Hukumar bada tallafin Karatu ta Jihar Kano Hon. Kabir Haruna Getso da gwamnan ya canza matsayin nashi ya zuwa sabon babban mai ba shi shawara kan harkokin samar da ayyuka na Jihar Kano.

Sauran waɗanda suka samu kansu a matakin mashawartan Gwamnan sun haɗa da Hon. Saleh Musa Sa’id da kuma Mr. Sylɓester Poul.

Da yake jawabi yayin taron rantsuwar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce yana matuƙar godiya ga Allah bisa ba mu damar ganin wannan rana da muke ciki na rantsar da waɗannan bayin Allah.

Gwamnan ya ce waɗannan bayin Allah da aka bai wa muƙamai a yanzu, an zaɓo su ne bisa cancanta bisa gaskiyarsu da riƙon amana.

“Zan yi amfani da wannan dama domin jan hankalin sabon Shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da magance cin hanci da rashawa da ya yi ƙoƙari wajen gudanar da aikin shi bisa gaskiya da riƙon amana.

“Ina so ka yi ƙoƙari wajen tuntuɓar tsohon shugaban wannan hukuma da ya kwashe lokaci yana jagoranci a wannan hukuma don shawarwari ma matuƙar amfani.

Gwamnan ya kuma buƙaci sabon Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen da ya zama mai kamantawa wajen gudanar da aikin shi, ba tare da sauraron wani ko wasu ba wajen gudanar da ayyukan da za su tsaftace ƙorafe-ƙorafe da jama’ar gari ke gabatarwa.

Haka kuma ya buƙaci sauran masu bashi shawara da aka rantsar da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukansu, bisa ƙoƙarin da suke a baya.

A nashi jawabin Hon. Kabir Haruna Getso ya ce suna matuƙar godiya bisa wannan dama da aka ba su kuma za su yi ƙoƙarin aiki ba tare da gajiyawa.

Shi ma Sabon Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe Alhaji Sa’idu Yahaya ya bada tabbacin cewa zai yi ƙoƙari matuƙa wajen ganin wannan nauyi da aka ɗora masa ya sauke don dawo wannan jiha bisa doro da ya kamata.

Haka zalika shi ma Hon. Sylɓester Poul ya bada tabbacin cewa zai aiki tuƙuru wajen haɗa kawunan al’ummar yankin Kudu wajen faɗakar da su tsarin da yake na gaskiya musamman tafiyar Kwankwasiyya.

By ukarofi