
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin Amurka sun faɗaɗa hanyoyin tantance sahihancin biza inda suka gabatar da tsarin bincika bayanan kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa, daga cikin sababbin dokokin akwai umartar ƴan waje da ke son shiga ƙasar bayyana baki ɗaya kafafen sada zumunta da suke amfani da su na tsawon shekaru biyar da suka gabata daga yanzu.
An sabunta tsarin ne da nufin binciken tabbatar da ba a taka dokokin shige da fice ba gabannin bada damar shiga ƙasar.
Ƙwararru akan harkar shige da fice sun ce duk wani yunƙuri na ɓoye wata kafa ta Soshiyal Mediya yayin binciken, zai iya haifar da hana bai wa mutum damar shiga ƙasar, sannan za a sanya shi a sahun waɗanda ake zargi da kuma haddasa masa jinkirin tafiya.
Daga cikin saƙonnin da ka iya haifar wa mutum matsala yayin zuwa ƙasar akwai wanda ke goyon bayan rikicin siyasa ko tawaye ga gwamnati a gida ko wajen ƙasar mutum.
Sai saƙon kalaman ɓatanci da na goyon bayan ta’addanci ko tsatstsauran ra’ayi da ke alaƙa da ƙungiyoyin ISIS, Al-Qaeda, Hamas ko Hezbollah, waɗanda dukkaninsu ka iya sa a hana mutum shiga.
Haka ma saƙonnin da ke nuna suka ga dokokin Amurka, shugabanninsu ko kuma al’adunsu, don haka wajibi ne ga mai son shiga a samu babu saƙon suka ga kowane ɓangaren da aka lissafo.
Bugu da ƙari, akwai saƙonnin da ke ɗauke da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, tarzoma, dabanci ko dukkanin wani haramtaccen saƙo.
Har’ilayau, akwai bada bayanai na ƙarya kamar suna ko ɓoye shafuka wanda ka iya sa a zargi mutum.
Sauran sun haɗa da saɓa wa dokokin shige da fice, barƙwanci da ka iya sa a fassara saƙonninsu ta wata fuska da dai sauransu.
