ADC ta ja hankalin ’yan Najeriya kan rijistar katin zaɓe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga ’yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yin rijista da karɓar Katin zaɓe na dindindin (PVC), domin tabbatar da rawar da ya dace su taka a dimokuraɗiyyar ƙasa.

Shugaban jam’iyyar na Gombe, Malam Ɗanladi Yau, ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin zartarwa na jiha da aka gudanar a Gombe ranar Juma’a.

Ya ce mallakar katin zaɓe ba kawai alhakin ɗan ƙasa ba ne, har ila yau shi ne babban makami da zai bai wa ’yan ƙasa damar canza makomar ƙasar.

“Abin da ya kamata mu fahimta shi ne, mallakar katin zaɓe nauyi ne a kan kowane ɗan ƙasa. Wannan shi ne abin da zai ba mu damar yin zaɓi na gaskiya domin samun canjin da muke buri,” in ji shi.

Ya”u, ya yi kira musamman ga matasa da suka kai shekaru 18 a kwanan nan da su shiga aikin rijistar don tabbatar da muradun su na dimokuraɗiyya sun samu dama.

A kan batun rikicin shugabanci a jam’iyyar, shugaban na ADC ya bayyana cewa shi ne sahihin shugaban da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta amince da shi, inda ya ce wa’adin tsohon shugaban jam’iyyar ya ƙare ne tun a 2019, sannan aka kore shi daga jam’iyyar a shekarar 2022.

Ya kuma jaddada biyayyarsa ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin David Mark, tare da bayyana cewa akwai shirin yin rajistar sabbin mambobi a dukkanin mazaɓu 114 na jihar Gombe, domin ƙarfafa jam’iyyar a matsayin babbar adawa ga APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

By ukarofi