
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa PDP, ta cimma matsayar tsayar da ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 daga yankin kudancin Nijeriya.
PDP ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Debo Ologunagba ta sanar da haka a ranar Litinin, yayin taron Majalisar Zartarwarta (NEC) karo na 102 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce, hakan ya biyo bayan jam’iyyar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓa-karɓa a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Bayelsa, Douye Diri.
Ya ƙara da cewa, NEC ta kuma tabbatar da tsarin karɓa-karɓa na Kwamitin Ayyukan jam’iyya (NWC) yayin fuskantar babban taronta a watan Nuwamba.
Kwamitin ya kuma nuna gamsuwa ga yadda ake cigaba da gudanar da shirye-shiryen taron.
