Zargin sauya akalar ₦6.5bn: Ba kumfar baki ake son ji ba, hujjoji za ku gabatar – Tsohon kwamishina ga Gwamnatin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’amarin zargin sauya akalar Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin Kano na neman ɗaukar wani salo yayin da tsohon Kwamishinan Labarai na zamanin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wato Muhammad Garba, ya zargi gwamnatin jihar da yin kumfar baki wajen yaɗa farfaganda a madadin gabatar da hujjoji.

A wata sanarwa da ya fitar wa manena labarai, tsohon kwamishinan ya yi tsokaci game da wata takarda da gwamnatin jihar ta fitar a ranar 25 ga Agusta, 2025 daga Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Ya ce, da fari bai so yin tsokaci akan al’amarin ba duba da cewa an miƙa shi zuwa ga kotu, inda daga bisani ya lura cewa akwai yunƙurin siyasantar da al’amarin da wasu matsaloli da ke cin karo da juna kan yadda gwamnatin ta ɗauki batun.

Ya bayyana cewa, tunda batun yana hannun kotu, ba buƙatar gwamnatin jihar ta cigaba da shiga gidajen jaridu tana ƙoƙarin kare kanta.

Muhammad Garba ya kuma tirje akan cewa abin tambayar ita ce ‘shin an cire kuɗaɗen ko kuma a’a’, yana mai cewa furucin gwamnatin na nuna neman kauce wa bada amsa game da tambayar.

Kazalika, ya zargi gwmanatin da ƙoƙarin ɗora wa tsohuwar gwamnati alhakin da bai shafe ta ba, yana mai cewa kurakuran baya ba za su zama hujja ta ƙin yin adalci ga gwamnatin ba a yanzu.

By Babaji