
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A halin yanzu tsohon kocin ƙungiyoyin Chelsea, Inter Milan, Manchester United da Tottenham, wato Jose Mourinho yana tsaka-mai-wuya a ƙungiyar Fenerbache da ke Turkiyya sakamakon ƙalubalen rashin nasara da ya ke fuskanta a matsayinsa na kocin ƴan wasan ƙungiyar.
Lamarin da ya jefa kocin mai shekaru 62 wanda ake kira da ‘Special One’ cikin mawuyacin hali da ka iya sa ya bar ƙungiyar.
Akan haka ne Nottingham Forest ta ƙasar Ingila ta sanya shi a sahun waɗanda za su maye gurbin Nuno Espirito matuƙar suki yi adabo da shi (Espirito) sakamakon tsamin dangantaka da ke tsakaninsa da mai ƙungiyar, wato Evangelos Marinakis.
Tsohon jami’in sanya ido kan al’amuran ƙungiyoyin Manchester United da Sunderland, Mick Brown ya shaida wa ‘Football Insider’ cewa ta yiwu Mourinho ya amsa koma horar da ƴan wasan Forest matuƙar ƙungiyar ta yi masa tayi duba da yadda yake da shirin koma wa aiki a gasar Premier League ta Ingila.
“Yana da wahala ya shafe sama da shekaru biyu ko uku a kowane kulob, don haka zai iya barin Turkiyya idan wata dama ta zo”, inji Brown.
