Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Umar Halilu ɗan shekara 29 da Abdullahi Salisu ɗan shekara 35 yan ƙauyen Dabaibayawa a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, yanzu haka suna hannun jami’an tsaro na farin kaya (Civil Defence).
Jami’an tsaron sun kama su ,suna ɗauke da wayar pole na wutan lantarki da ba a san adadin su ba lokacin da suke ƙoƙarin kama masu sayen.
Kwamandan hukumar Aminu Datti Ahmad yaba da ƙoƙarin haɗakar tsaro bisa wannan na mijin ƙoƙari da suka yi.
Ya ce jami’an sa na nan ba dare ba rana wajen sa ido wajen masu ƙoƙarin zagon ƙasa da kayan gwamnati musamman ɓarayin wayar wutan lantarki a manyan hanyoyi da ke faɗin jihar.
Yayi kira ga al’ummar jihar da su ba jami’an tsaron goyon baya wajan yaƙi da miyagun ayyuka a jihar.
