Yanzu-yanzu: Tsohon Kwantirola Janar na Kwastom, Ahmed Aliyu Mustapha ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Kwantirola Janar na Hukumar Kwastom (NCS), Ahmed Aliyu Mustapha ya rasu.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya tabbatar da rasuwar a wani rubutu ta kafar X a yau Alhamis.

Ya nuna kaɗuwarsa game da rashin tsohon babban jami’in inda bayyana shi a matsayin jajirtacce wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Mustapha, wanda yaya ne ga Lamiɗon Adamawa, Dakta Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustapha, ya kuma taɓa riƙe muƙamin Sardaunan Adamawa.

Marigayin ya shiga aikin Kwastom ne a matsayin ƙaramin jami’i inda ya yi ta samun ƙarin girma har yakai ga an naɗa shi Kwantirola Janar a shekarar 1999.

Ya bada gagarumar gudumawa wajen daƙile ayyukan fasa-ƙwauri da yin zagon-ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa.

Haka kuma ya yi ritaya a shekarar 2003 bayan shafe sama da shekaru 30 a aikin.

By Babaji