ALGON ta ziyarci ƙananan hukumomin Filato da jaddada goyon baya ga Gwamna Mutfwang

Spread the love

Daga HABU Ɗan SARKI a Jos

Reshen ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ya sake jaddada cikakkiyar sadaukarwarsa wajen bunƙasa dukkanin ƙananan hukumomi a dukkan faɗin jihar, tare da sake jaddada goyon baya ga jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang wanda suka ce yana kawo sabbin sauye-sauye na cigaba a jihar.

Shugabannin ƙananan hukumomi guda 17 sun bayyana cewa gwamnatin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ta samar musu da kyakkyawan yanayi da nuna jagoranci nagari, ƙwarewa a harkar shugabanci, da inganta rayuwar mutanen karkara, wanda yake daga cikin ƙudirorin gwamnati mai ci a Jihar Filato.

Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin da ƙungiyar ta kai ziyarar gani da ido ga wasu ƙananan hukumomi da ke yankin Kudancin Filato, domin ƙarfafa gwiwar shugabannin kan samar da ayyukan raya ƙasa da shugabanci nagari.

Shugaban ALGON na Jihar Filato, Hon. Hamisu Anani, wanda kuma shi ne Shugaban hukumar ƙaramar hukumar Wase, ya bayyana cewa wannan ziyara ta haɗa da zuwa ƙananan hukumomin Qua’an-Pan, Mikang, da kuma Langtang Kudu, inda suka tattauna sosai da ýan majalisun yankunan da masu riƙe da sarautun gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce, manufar wannan aikin rangadi da suke yi shi ne ƙarfafa haɗin kai don cigaba, gina haɗin gwiwa, magance manyan ƙalubalen shugabanci, da cike giɓin da ake samu a tsarin tafiyar da shugabancin ƙananan hukumomi.

“Mun kewaya ƙananan hukumomi 17 da muke da su, domin duba aikace-aikace da aka gudanar na gyaran ofisoshi da ƙauyuka daban-daban,” in ji Anani. “Shugabancin ƙananan hukumomi na da ginshiƙai uku masu muhimmanci—reshen zartarwa, reshen majalisa, da sarakunan gargajiya. Idan duk sun yi aiki tare, cigaban da ake burin samu a nan Filato zai tabbata.”

Yayin da yake nuna godiya ga goyon bayan da Gwamna Mutfwang yake ba su, Shugaban ALGON ya amince cewa duk da ƙarancin kayan aiki, shugabannin ƙananan hukumomi sun samu nasarar aiwatar da ayyuka masu yawa da za su yi tasiri mai ɗorewa ga al’ummominsu.

Ya nemi haɗin kai da addu’a domin samun nasara akan ayyukan da suka sa a gaba a duk matakai, tun daga unguwanni, ƙananan hukumomi, da jihar, yana mai cewa, “Dole mu haɗa hannu wajen tallafa wa hangen nesan da gwamnati ke yi na samar da muhimman canje-canje a Jihar Filato.”

Anani ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomi kan nasarorin da suka samu a ayyukan da suke kan aiwatarwa da waɗanda suka ƙammala a ƙananan hukumomin su, inda ya tabbatar wa jama’a cewa yankin kudancin jihar na samun kulawa ta musamman daga Gwamna, kuma nan ba da daɗewa ba za a fara aiwatar da wasu manyan ayyuka a wannan yanki a mataki na gaba na ayyukan gyaran hanyoyi da za a gudanar.

Shugabannin ƙananan hukumomin Qua’an-Pan, Mikang, Langtang ta Kudu, da Shendam, Hon. Christopher Audu Wallet, Hon. Bernard Alkali, Hon. Nanfa Nbin, da Hon. Nicholas Kemi Nshe—sun nuna ƙwarin gwiwar su wajen samar da ayyuka masu muhimmanci, don jama’ar su su samu cin moriyar mulkin dimukraɗiyya daga tushe.

Sun bayyana kansu a matsayin jakadun gwamnati ga Gwamna Mutfwang, suna masu ƙara jaddada ayyukan da suka gabatar da suka haɗa da sabbin ofisoshi, da gyaran asibitoci, makarantu, da hanyoyi a matsayin hujjojin ayyukan cigaba a ƙarƙashin gwamnatin PDP a jihar.

Shugabannin sun yi alƙawarin cigaba da ɗaukar matakai wajen magance matsalolin cigaba a yankunan su, kuma ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har sai an cimma nasarorin da ake buƙata don moriyar jama’a.

Kwamitin haɗin gwiwar ma’aikata, da sauran masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomin sun yabawa Gwamna Caleb Mutfwang da shugabanninsu kan tanadin taki da kayan aikin gona da aka tallafa musu da su a kan lokaci cikin wannan shekara, tare da kiran da a ƙara faɗaɗa tsarin shugabanci na haɗin gwiwa da ake da shi a yankunan.

A yayin wannan ziyara, shugabannin hukumomin sun fara da ziyarar sarakunan gargajiya a masarautun su kafin su haɗu da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka bayyana dalilin gudanar da wannan binciken.

Mai Martaba Long Gamai na Shendam; Miskoom Martins Shaldas, da Long-Tehl na masarautar Tehl Donald Puntel na Mikang, da Miskoom Safiyanu Allahnanan, mai riƙon sarautar Long Pan na Qua’anpan, tare da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya, sun karɓi shugabannin hannu biyu-biyu. Sun kuma yaba da wannan yunƙuri nasu tare da ba da cikakken goyon baya a matsayin masu kula da al’adu da sarautun gargajiya.

Sun roƙi shugabannin su fifita tsaron rayukan al’umma da dukiyoyi, suna masu jaddada cewa lafiyar al’umma ta dogara ne da kyakkyawan haɗin kai dake tsakanin sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki.

Sarakunan gargajiya sun bayyana cewa wannan ziyara ta gani da ido a matsayin irin ta farko a Jihar Filato, tun bayan dawowar dimukraɗiyya.

By ukarofi