
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fenerbahce ta kori mai horarawa Jose Mourinho bayan aikin shekara ɗaya da ‘yan watanni.
Tafiyar ɗan ƙasar Portugal ɗin ta zo ne kwana biyu bayan kulob ɗin ya kasa samun gurbi a gasar zakarun Turai ta Champions League, inda Benfica ta cire su a wasannin neman gurbi.
Cikin wata sanarwa, Fenerbahce ta ce Mourinho “ya bar kulob ɗin” kafin daga baya ta gode wa mai shekara 62 ɗin. Daga baya wani jami’i a kulb ɗin ya faɗa wa BBC cewa korarsa suka yi.
Mourinho, wanda ya horar da ƙungiyoyi 10 ciki har da Chelsea da Real Madrid da Manchester United da Tottenham, ya jagoranci Fenerbahce ta Turkiyya wajen ƙarewa a mataki na biyu a babbar gasar Turkiyya ta Super League a kakar wasa ɗaya da ya yi, kamar yaddaBBC Hausa ta ruwaito.
Mourinho ya sha sukar alƙalan wasan Turkiyya, har ma an taɓa dakatar da shi wasa huɗu – wanda aka rage zuwa biyu – game da kalaman da ya yi kan alƙalan wasa bayan wasansu da babbar abokiyar hamayya Galatasaray.
