Yadda Son da Muller suka fara nuna bajinta a Amurka

Spread the love

Tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar Tottenham ta Ingila, Son Heung-min da da tsohon kyatfin ɗin ƙungiyar Bayern Munich ta Jamus Thomas Muller sun fara taka leda da ƙafar dama a gasar Amurka ta Major League Soccer, inda suka fara da zura ƙwallo a wasannin da suka buga a ranar Asabar.

Son ɗan asalin ƙasar Koriya ta Kudu mai shekara 33 ya jefa ƙwallo ne a bugun tazara a minti shida da shigarsa filin wasa domin fara taka leda a ƙungiyar Los Angeles FC a gasar MLS, inda aka tashi wasan 1-1 da ƙungiyar FC Dallas.

ƙungiyar ta kafa tarihin cinikayya mai tsada wajen ɗauko shi a kan fam miliyan 20 daga Tottenham inda ya yi sama da shekara 10 yana murza leda.

“Na yi farin cikin zura ƙwallo a wasana na farko a MLS, amma na fi murna da samun maki ɗaya da muka yi.”

A ɗaya ɓangaren kuma, Muller mai shekara 35 ya zura ƙwallo ne a bugun fanareti, inda ƙungiyarsa ta Vancouver Whitecaps ta doke St Louis City da ci uku da biyu.

By ukarofi