Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci wasu bankunan kasuwanci guda shida a Nijeriya da su bai wa Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun cikakkun bayanan kuɗi na asusun banki da ke da alaƙa da ɗan gwagwarmaya, ɗan siyasa, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore da kamfanoninsa.
Umarnin wanda mai shari’a Emeka Nwite ya bayar a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya biyo bayan ƙarar da lauyan ‘yan sanda, Wisdom Madaki, ya gabatar a gaban kotun a madadin Sufeto Janar.
Wannan lamari dai wani sabon babi ne na taƙaddamar shari’a da ta dabaibaye Sowore, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma mai fafutukar neman kawo sauyi a yanzu, wanda ya daze yana sukar gwamnatocin Nijeriya da suka shuɗe.
A cikin bayanan da kotu ta shigar, an gano aƙalla asusun banki 26 da ke da alaƙa da Sowore. Waɗannan sun haɗa da asusun na Sahara Reporters Media Foundation, da tsarin siyasarsa, African Action Congress (AAC), da sauran ƙungiyoyi masu alaƙa.
Buƙatar Sufeto Janar ta nemi a bai wa bankuna “umarnin gabatar da bayanan asusu tare da lambobin asusun Sowore daga Janairun 2024 zuwa yau.”
A cikin takardar goyon bayan, rundunar ‘yan sandan ta ce ana binciken Sowore ne da laifin bayar da kuɗaɗen ta’addanci, halasta kuɗaɗen haram, da kuma ayyukan damfara.
Sanarwar ta bayyana cewa rahotannin leƙen asirin da ake zargin sun alaƙanta harkokin kuɗi na Sowore da kuɗaɗen ta’addanci.
“Ofishin wanda ya shigar da ƙarar ya karɓi rahoton sirri cewa wanda ake ƙara na farko yana amfani da asusun ne don tallafawa ayyukan ta’addanci, halatta kuɗaɗen haram, kuma yana samun tallafin kuɗi daga abokan hulɗar ƙasashen waje don ta’addanci,” inji Sufeto Janar.
Rundunar ‘yan sandan ta ce tabbatar da bayanan asusun bankin ya zama dole don ci gaba da gudanar da bincike kan harkokin kuɗi da ake zargin Sowore ya yi.
Rundunar ‘yan sandan ta ci gaba da cewa, Sowore ya yi amfani da asusu na banki da dama wajen tafiyar da wasu kuɗaɗe da ake tuhuma da kuma samun tallafin kuɗi daga ƙasashen waje, lamarin da ke nuni da tsarin zamba da kuɗaɗe masu alaƙa da ta’addanci.
“Wanda ake ƙaran ya kasance yana amfani da asusun ne wajen hada-hadar kuɗi, tallafin ta’addanci, da kuma ayyukan damfara,” inji sanarwar.
Yayin da ‘yan sanda ba su bayar da cikakkun bayanai game da waɗanda ake zaton masu kuɗi daga ƙasashen waje, sun dage cewa samun bayanan banki na Sowore na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da rahotannin leƙen asirin.
Tare da umarnin kotu a yanzu haka, bankunan shida sun wajabta wa IGP cikakken bayanin da aka nema wanda ya shafi duk wani ciniki da ke da alaƙa da Sowore da ƙungiyoyin sa daga Janairu 2024 zuwa Agusta 2025.
Rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana ko za a tuhumi Sowore a hukumance ba, amma majiyoyi sun nuna cewa takardun kuɗi za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance mataki na gaba na binciken.
Sowore, wanda aka kama tare da tsare shi sau da yawa a Nijeriya tun a shekarar 2009, ya sha zargin hukumomi da kai masa hari saboda fafutuka da aikin jarida na bincike.
Har yanzu dai Sowore bai bayar da amsa a hukumance ba kan hukuncin kotun ba.
