Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta fitar da sanarwar faɗakar da jama’a game da yaɗuwar jabun maganin Postinor-2 (Leɓonorgestrel 0.75mg) maganin hana ɗaukar ciki a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce magungunan jabun waɗanda aka bayyana sunayensu da nau’in 1 da nau’in 2 na bogi ne, an sanya su ne bayan ƙungiyar Society for Family Health (SFH), mai izinin shigo da kayayyaki, ta tabbatar da cewa ba ta shigo da waɗannan kayayyakin ba.
NAFDAC ta bayyana cewa fakitin jabun na ɗauke da kura-kurai da dama, waɗanda suka haɗa da tambarin tabbatar da kuskuren rubuta “ɓeify” maimakon “ɓerify” da kuma wata jumla da aka buga ba daidai ba “Rarrabawa a Nijeriya” a bayan fatikin.
Ya ce, “Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) tana sanar da jama’a game da yaɗuwar jabun nau’i na 1 da 2 na maganin POSTINOR 2 (Leɓonorgestrel 0.75mg) da ke yawo.
Hukumar NAFDAC ta tabbatar da cewa wasu jabu biyu na Postinor-2 suna yaɗuwa. Sun haɗa da samfuri na jabu (Nau’i 1), Batch T36184B, wanda aka ƙera a watan Agusta 2024 tare da ranar ƙarewa a Agusta 2028, da samfuran jabu (Nau’in 2), Batch 332, wanda aka ƙera a cikin Maris 2023 tare da ranar ƙarewa na Fabrairu 2027. Dukansu suna ɗauke da lambar rajista 8.04-6.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa magungunan jabu na iya kunshe da sinadaran da ba daidai ba ko masu cutarwa, da sinadarin leɓonorgestrel da bai dace ba, kuma ana iya samar da su a cikin yanayi mara kyau, wanda ke haifar da babbar illa ga lafiyar jama’a.
Hukumar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano inda aka samu gurɓatattun kayayyakin, yayin da aka umurci daraktocinta na shiyyoyin da ko’odinetocinta na jihohi da su gudanar da sa ido tare da kawar da maganin a faɗin ƙasar.
An kuma shawarci masu saye da sayar da lafiya da su bincika a hankali lambobi na PIN, da bayar da rahoton duk wani samfuran da ake zargin na jabu ne, kuma a koyaushe su sayi magunguna daga ingantattun hanyoyi.
