Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Adewale Adeniyi, ya jaddada ƙudirin hukumar na ƙara yin haɗin gwiwa da Hukumar ‘Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Nijeriya (NACCIMA) domin inganta harkokin kasuwanci, samar da kuɗaɗen shiga, da kula da iyakoki.
Adeniyi ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Agusta, 2025, yayin da ya karɓi baƙuncin zaɓaɓɓen shugaban hukumar NACCIMA na ƙasa, Jani Ibrahim, da tawagarsa a hedikwatar hukumar kwastom da ke Maitama, Abuja.
Da yake maraba da tawagar masu zaman kansu, shugaɓan Kwastom ya nuna jin daɗinsa ga yabon hukunar NACCIMA da kuma amincewa da sauye-sauyen da hukumar kwastom ta yi.
Ya kuma bayyana cewa, tun farko, mulkinsa ya ba da fifikon haɗin gwiwa a matsayin hanyar samun kuɗaɗen shiga, tsaron ƙasa, da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
“Lokacin da na shiga ofis, ɗaya daga cikin abubuwan farko da na yi niyya a kai shi ne batun haɗin gwiwa, kuɗaɗen shiga da tsaro na da muhimmanci, amma don samun nasara a duka biyun, dole ne mu ƙarfafa harkokin kasuwanci,” inji CGC Adeniyi.
Ya ƙara da cewa, “A yau, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, muna kan gaba tare da wannan haɗin gwiwa, kuma za mu sadaukar da tebura na musamman ga mambobinku don warware batutuwan da suka shafi aiwatar da ayyukanmu.”
A nasa jawabin, shugaban NACCIMA, Jani Ibrahim ya taya Adeniyi murnar zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban hukumar kwastom ta duniya, yana mai bayyana shi a matsayin “mutumin da ya cancanci karramawa ga ci gaban shugabancin Nijeriya a hukumar kwastom.”
