Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ‘yan sanda a Anambra ta ƙaddamar da bincike kan rahoton wani matashi da ake zargin mahaifinsa ya ɗaure shi da sarƙa tsawon shekaru biyar a Igboukwu da ke ƙaramar hukumar Aguata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Awka.
Ikenga ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ɗansa ya fita ƙasar waje ba tare da izini ba, wanda hakan ya sa ya tsare shi bayan ya dawo.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sanda, Ikioye Orutugu, ya umurci jami’an da su gaggauta gudanar da bincike kan rahoton da ke yawo a kafafen yaɗa labarai.
Mutumin da aka ɗaure mai suna Chogbo, wanda aka fi sani da Agudo, an bayyana cewa mahaifinsa ya ɗaure shi da sarƙa har tsawon shekaru biyar bisa dalilin tafiya ƙasar waje ba tare da izini ba.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike na farko don tabbatar da gaskiya da kuma kare lafiyar wanda aka azabtar. Inda aka tabbatar da laifin, waɗanda ke da alhakin za su fuskanci doka,” inji Ikenga.
Ya tabbatar da cewa an ceto wanda abin ya shafa kuma yana samun kulawar da ta dace.
Rundunar ta yaba wa matasan unguwa da suka bankaɗo lamarin, inda ta bayyana shigarsu a matsayin abin yaba wa na haɗin gwiwar al’umma wajen aikin ‘yan sanda.
Ikenga ya bada tabbacin cewa sakamakon binciken zai fito fili.
