NAHCON ta fitar da tsarin harkokin Hajjin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da ranakun kammala shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2026.

NAHCON ta bayyana haka ne a shafinta na X ranar Juma’a, inda ta ƙulla yarjejeniya ta MoU tsakaninta da hukumomin Saudiyya cewa za a fara shirye-shiryen hajjin a watan Nuwamban 2025.

Ta ce, zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2026 za a rufe biyan kuɗin rajistar zuwa aikin hajji ga maniyyata.

Daga nan a ranar 1 ga Fabarairu, 2026 kuma za a rufe shigar da kwangilolin sufuri da masauki a shafin yanar gizo na Nusuk Masar.

Hukumar ta kuma ce a ranar 20 ga Maris, 2026 za a kammala bada biza ga maniyyatan, tana mai jaddada cewa babu ƙarin lokaci akan haka da za ta yi.

Bugu da ƙari, NAHCON ta bada wa’adin 8 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za ta kammala raba kujerun hajji da za ta ba kowace jiha.

Daga ƙarshe, ta kirayi maniyyata da hukumomin alhazan jihohi da kiyaye sharuɗɗa da tsare-tsaren da zayyano ta yadda za gudanar shirye-shiryen bisa tsari da inganci.

By Babaji